APC na da shirin ci gaba da rike madafun iko na tsawon shekaru 32, in ji Buni

APC na da shirin ci gaba da rike madafun iko na tsawon shekaru 32, in ji Buni

- Gwamnan jihar Yobe ya bayyana manufar jam'iyyar APC ta kasanceewa a mulki har shekaru 32

- Ya bayyana cewa, jam'iyyar na da shirin da zai sa ta zauna daram a karagar mulki na wa'adi da yawa

- Ya kuma jaddada manufar jam'iyyar na ci gaba da samar da romon dimokradiyya ga 'yan Najeriya

Shugaban riko na kwamitin tsare-tsaren babban taron kasa na jam'iyyar APC kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya ce jam'iyyar na kokarin ganin ta ci gaba da mulki a kalla na tsawon shekaru 32, Daily Nigerian ta ruwaito.

Mista Buni ya bayyana hakan ne lokacin da yake kaddamar da kwamitin tuntuba da dabaru na jam’iyyar na mambobi 61, a Sakatariyar APC ta Kasa, da ke Abuja, a ranar Talata.

KU KARANTA: An ba da belin mawakin yabo da ya sake wakar yabo da ba a tantance ba

APC na da shirin ci gaba da rike madafun iko na tsawon shekaru 32, in ji Buni
APC na da shirin ci gaba da rike madafun iko na tsawon shekaru 32, in ji Buni Hoto: businessday.ng
Asali: Facebook

A cewarsa, ya kamata jam'iyyar ta kasance a kan mulki don ci gaba da samar da romon dimokiradiyya da take gabatarwa tun daga shekarar 2015.

Ya bayyana cewa jam'iyyar ta yanke shawarar kafa kwamiti mai karfin gaske don tsara dabaru da shiri tsaf don aiwatar da wannan manufar.

Gwamnan ya ce, “Don haka kundin tsarin dabaru da tuntuba, shi ne ya karfafa nasarorin da muka samu wajen gina jam’iyya mai karfi tare da ingantaccen tsari wanda zai cika APC don fuskantar kowacce jarabawa a kowane lokaci.

“Burinmu shi ne samar da wata dabarar da za ta tsayar da jam’iyyar daram har ta wuce wa’adi na 6, 7 da ma 8 na mulki don aiwatar da manufofin jam’iyya yadda ya kamata, inganta rayuwar 'yan Najeriya da kuma, ci gaba da kasancewa jam'iyyar siyasa ta Najeriya.:

KU KARANTA: 'Yan bangan Amotekun sun sake kame wasu shanu sama da 300

A wani labarin daban, A kokarin farfado da tattalin arzikin kasa, gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari a Najeriya ta karbo bashin naira biliyan daya domin taimakawa masu kananan masana'antu, BBC ta ruwaito.

An karbo bashin ne ta hannun bankin masana'antu karkashin Ma'aikatar kasuwanci masana'antu da zuba hannayen jari ta kasar.

Adeniyi Adebayo na ma'aikatar ne ya bayyana hakan yayin wani shiri na karfafawa kananan masana'antu da aka yi.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel