Bakuwar cuta a Kano: FG ta aika da rundunar taimakon gaggawa zuwa Kano

Bakuwar cuta a Kano: FG ta aika da rundunar taimakon gaggawa zuwa Kano

- Biyo bayan kara kamarin wata cuta da ta bullo a jihar gwamnatin tarayya ta tura taimakon gaggawa

- Rundunar taimakon gaggawan za ta binciki musabbabin cutar tare da zakulo mafita gare ta

- Hukumar NCDC da NAFDAC na ci gaba da gudanar da bincike don tattara bayanan musabbabin cutar

Gwamnatin Tarayya ta tura Rundunar Taimakon Gaggawa zuwa Jihar Kano don gano abin da ke boye na rashin lafiya tare da kula da wadanda suka kamu a cikin jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Darakta-Janar na Cibiyar hana yaduwar Cututtuka ta Najeriya, Chikwe Ihekweazu, ya bayyana hakan a Abuja a ranar Litinin a taron hadin gwiwa na kasa da aka yi game da Kwamitin Shugaban kasa kan Korona.

Rahotanni sun ce mutane hudu sun mutu tare da wasu sama da 200 da suka kamu da wannan bakuwar cutar da aka tabbatar a kananan hukumomi 13, ciki har da kananan hukumomi takwas na birnin jihar.

KU KARANTA: Saura kiris a fara biyan masu aikin sufuri tallafin kudi na 'Survival Fund'

Bakon cuta a Kano: FG ta aika da tallafin gaggawa zuwa jihar Kano
Bakon cuta a Kano: FG ta aika da tallafin gaggawa zuwa jihar Kano Hoto: ncdcgov
Asali: Instagram

Ihekweazu ya ce Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano ta ba da rahoton tarin mutane a kananan hukumomi 13 na jihar inda mafi yawan masu dauke da zazzabi, amai, sauyawar idanu zuwa kalan rawaya da kuma ciwon ciki a matsayin alamomi.

“Mun gwada samfura guda hudu da aka dauka daga wadannan cututtukan don gwajin zazzabin Lassa da zazzabi a babban dakin gwajin kasa na NCDC. Sakamakon ya fito ba abinda ake zargi bane.

"Muna aiki tare da, 'yar'uwarmu hukumar NAFDAC da kuma wani masanin guba daga FMoH don yin gwaji kan abubuwan da ba za su iya kamuwa ba," in ji shi.

Ya ce hukumar ta kuma tattara karin samfurin mutane da na muhalli don gudanar da gwajin asalin inda cutar ta bullo da dalilin bullowarta.

Ya ce, “Babban abin da muke maida hankali shi ne gano musabbabin wannan cutar, tabbatar da kula da lamuran yanzu da kuma kula da yaduwar cutar.

"Za mu ci gaba da fadakar da jama'a game da abubuwan da muka gano, yayin da muke goyon bayan martanin jihar."

KU KRANTA: Fayose ga Buhari: Ka bai wa 'yan Najeriya kunya da alkawuranka

A wani labarin daban, Gwamnatin jihar Kano ta haramta sayar da sinadarin dan tsami da danginsa a fadin jihar baki daya, biyo bayan wata cuta da ake zargin sinadarin ya haifar ga jama'a.

Shugaban hukumar kare hakkin masu sayan kayayyaki Baffa Babba Dan Agundi ne ya bayyana hakan a hirar da ya yi da BBC.

Baffa ya ce bincike ya nuna cewa wadannan sinadaran da ake hada kayan shaye-shaye da su da yawansu lokacin ingancinsu ya kare, don haka babu mamaki dan an ce suna cutar da masu amfani da su.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Tags: