Sojojin Najeriya sun yi kaca-kaca da haramtacciyar matatar mai a Abia

Sojojin Najeriya sun yi kaca-kaca da haramtacciyar matatar mai a Abia

- Sojojin Najeriya sun bankado wata haramtacciyar matatar man fetur dake aiki a jihar Abia

- Sojojin sun afkawa matatar, yayin da suka lalata ta suka kuma fatattaki ma'aikatanta a cikinta

- Sun samu nasarar kwato motoci da wasu kayayyakin aikin tace danyen man fetur a matatar

Mazajen runduna ta 14 ta sojojin Najeriya a Ohafia da ke hade da hedikwatar bataliya ta 144 a karamar hukumar Ukwa ta Yamma ta jihar Abia sun lalata haramtacciyar matatar mai da ke Ukwa ta Gabas.

Wakilin jaridar The Nation ya tattaro cewa matattarar matatar tana aiki ne ta wata dabar danyen mai da ke aiki tsakanin Abia da jihar Ribas.

Wasu majiyoyi sun shaida cewa ba wanda aka kama sannan kuma an tabbatar da kwacewa tare da lalata wasu motocin bas kirar L300 biyu, danyen mai da kuma tankokin da ake amfani da su wajen dafa haramtaccen danyen mai da aka sace daga bututun NNPC a yankin.

KU KARANTA: Fayose ga Buhari: Ka bai wa 'yan Najeriya kunya da alkawuranka

Sojojin Najeriya sun yi kaca-kaca da haramtacciyar matatar mai a Abia
Sojojin Najeriya sun yi kaca-kaca da haramtacciyar matatar mai a Abia Hoto: crimefacts.news
Asali: UGC

Majiyar ta bayyana cewa an gudanar da aikin da ya kai ga lalata haramtacciyar matatar ne tare da hadin gwiwar jami'an tsaro na DSS a Owaza dake karamar hukumar Ukwa ta Yamma.

Sun kara da cewa; “Mun samu masaniya game da ayyukan haramtacciyar dabar danyen mai da ke aiki tsakanin Abia da Jihar Ribas.

“Daga bayanan da muka samu, mun bi su zuwa ga al’ummar Nkali a cikin jihar Ribas inda muka gano sansaninsu na tace mai ba bisa ka’ida ba.

“Babu wanda aka kama. Wurin yana da damshi. Abin da ya faru shi ne, da farko sun hango mu sai suka tsere kuma saboda wurin yana da damshi, ya ba mu wahalar iya bin su.”

KU KARANTA: APC na da shirin ci gaba da rike madafun iko na tsawon shekaru 32, in ji Buni

A wani labarin, Wasu 'yan Najeriya sun fara bayyana adawarsu da rashin jin dadi ga shirin gwamnatin tarayya na kashe zunzurutun kudi har Dala Biliyan guda da rabi, domin gyara matatar man fetur mafi dadewa a kasar ta Fatakwal da ke jihar Rivers.

Majalisar zartarwa ta kasa ta amince da fitar da wadannan kudade don yin gagarumin aikin a ranar Laraba da ta gabata.

Ita dai wannan matata ta shafe fiye da shekaru 50 tana aiki, kafin fara samun matsala a shekarun baya bayan nan, lamarin da ake ganin ya haifar da gagarumin cikas wajen tace man a cikin gida.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel