Tukuicin sauya sheka:Omisore, Bankole, Dogara sun samu manyan mukamai a APC

Tukuicin sauya sheka:Omisore, Bankole, Dogara sun samu manyan mukamai a APC

- APC ta nada wani kwamiti na mutum 61 gabanin babban taronta na kasa mai zuwa

- Za a kaddamar da kwamitin a ranar Talata, 23 ga Maris, a Abuja

- A cewar rahoton, kwamitin zai sake dawo da APC a zukatan ‘yan Najeriya

Tsohon shugaban kwamitin majalisar dattijai kan kasafin kudi, Iyiola Omisore, tsoffin kakakin majalisar wakilai guda biyu, Dimeji Bankole da Yakubu Dogara sun samu mukamai a APC.

Jiga-jigan na jam'iyya mai mulki sun samu shiga cikin kwamitin mutum 61 da APC ta sanar a matsayin na tuntuba a ranar Litinin, 22 ga watan Maris.

Legit.ng ta tattaro cewa sanya su cikin jerin mutanen baya rasa nasaba da dawowar su jam’iyyar APC, bayan sauya sheka daga jam’iyyun SDP, ADP da PDP.

Tukuicin sauya sheka:Omisore, Bankole, Dogara sun samu manyan mukamai a APC
Tukuicin sauya sheka:Omisore, Bankole, Dogara sun samu manyan mukamai a APC Hoto: @DrIyiolaOmisore, @YakubDogara
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Kada ‘yan Najeriya su sanya siyasa a harin da aka kai mun, in ji Ortom

Wata sanarwa daga John James Akpanudoehede, sakataren Kwamitin Kula da Shirye-shiryen Babban Taron jam’iyyar na kasa, ta ce Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ne zai kaddamar da kwamitin a ranar Talata, 23 ga watan Maris.

Gwamnan jihar Jigawa, Abubakar Badaru zai kasance shugaban kwamitin yayin da Ikechi Emenike zai kasance a matsayin sakatare.

An tattaro cewa kwamitin, a cikin sauran abubuwa, zai bullo da dabarun da za su sanya jam’iyya ya samu babban matsayin a cikin jama’a sannan kuma ya tsara lokaci da tsarin aiwatar da shawarwarin ta.

Mambobin kwamitin sune:

1. H.E. Mohammed Badaru Abubakar – Ciyaman

2. H.E. (Sen.) Obarisi Ovie Omo-Agege – Mamba

3. H.E. Alh. Yahaya Bello – Mamba

4. H.E. Prof. Babagana Umar Zulum – Mamba

5. H.E. Alh. Inuwa Yahaya – Mamba

6. H.E. Engr. Abdullahi Sule – Mamba

7. H.E. (Hon) Aminu Bello Masari – Mamba

8. H.E. Simon Bako Lalong – Mamba

9. H.E. Babajide Sanwo-Olu – Mamba

10. H.E. Dapo Abiodun – Mamba 11. H.E. (Sen.) Hope Uzodinma – Mamba

12. H.E. David Nweze Umahi – Mamba

13. H.E. Alhaji Abdullahi Umar Ganduje – Mamba

14. H.E. (Sen.) Aliyu Magatakarda Wammako – Mamba

15. H.E. (Sen.) Mohammed Danjuma Goje – Mamba

16. H.E (Sen.) Kashim Shettima – Mamba 17. H.E. (Sen.) Ibikunle Amosun – Mamba

18. H.E. (Sen.) Mohammed Umar Jibrilla – Mamba

19. H.E. Timipre Sylva – Mamba

20. H.E. Rauf Aregbesola – Mamba

21. H.E. (Dr) Chris Ngige – Mamba

22. H.E. (Sen) George Akume – Mamba

23. Abubakar Malami, SAN – Mamba

24. Hajia Sadiya Umar Faruq – Mamba

25. Mallam Adamu Adamu – Mamba

26. H.E. Akinwunmi Ambode – Mamba

27. H.E. Mohammed A. Abubakar – Mamba

28. H.E. (Sen.) Mohammed Adamu Aliero – Mamba

29. H.E. Gbenga Daniel – Mamba

30. H.E. Sullivan Chime – Mamba

31. H.E. (Sen.) Iyiola Omisore – Mamba

32. H.E. Mamadu Aliyu Shinkafi – Mamba

33. H.E. Saidu Dakingari – Mamba

34. Rt. Hon. Dimeji Bankole – Mamba

35. Rt. Hon. Yakubu Dogara – Mamba

36. Sen. Julius Ali Ucha – Mamba

37. Sen. Ganiyu Solomon – Mamba

38. Sen. Margaret Okadigbo – Mamba

39. Sen. Jibrin Wowo – Mamba

40. Sen. Anthony Oduma Agbo – Mamba

41. Sen. Robert Ajayi Boroffice – Mamba

42. Sen. Mohammed Sani Musa – Mamba

43. Sen. Khairat Gwadabe – Mamba

44. Hon. Nkeiruka Onyejeocha – Mamba

45. Hon. Abdulrahman Kawu Sumaila – Mamba

46. Hon. Usman Mohammed – Mamba 47. Mallam Nuhu Ribadu – Mamba

48. Hon. Abubakar Lado Suleja – Mamba

49. Hon. Makinde Peter Abiola – Mamba

50. Hon. Blessing David Onuoha – Mamba

51. Alhaji Kashim Imam – Mamba

52. Misis Mimi Drubibi Adzape – Mamba

53. Olorugun Emerhor Ortega – Mamba 5

4. Obong Umana Okon Umana – Mamba

55. Prince B.B Apugo – Mamba

56. Chief Ify Ugo Okoye – Mamba

57. Hon. Abike Dabiri-Erewa – Mamba

58. Hajia Hadiza Bala Usman – Mamba

59. Princess (Hon) Miriam Onuoha – Mamba

60. Ideato C. Ideato Okoli – Mamba

61. Dr. Ikechi Emenike – Sakatare

KU KARANTA KUMA: Kada ku yarda a kafa dokar halasta sanya Hijabi a makarantu, CAN ga yan majalisa Kiristoci

A wani labarin, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya bayyana cewa abokan aikinsa sun damu a dalilin harin da aka kai wa takwaransu, Samuel Ortom.

Jaridar This Day ta rahoto Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya na wannan bayani ne a ranar Litinin, 22 ga watan Maris, 2021, a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Mai girma Abdullahi Umar Ganduje ya nuna cewa ya na sa rai kwanan nan za a kawo karshen matsalar rashin tsaron da ake fuskanta a bangarorin Najeriya.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng