Kada ‘yan Najeriya su sanya siyasa a harin da aka kai mun, in ji Ortom

Kada ‘yan Najeriya su sanya siyasa a harin da aka kai mun, in ji Ortom

- Gwamna Samuel Ortom ya roki da kada su siyasantar da harin da aka kai masa, yana mai cewa hakan ya wuce siyasar bangaranci

- Ortom ya bayyana cewa ba shine gwamna na farko da aka kaiwa hari ba kuma cewa yana iya zama wani a gaba

- Sai dai kuma duk da haka, Gwamna Ortom ya ce akwai wasu Fulani masu kishin kasa domin ba a taru an zama daya ba

Gwamnan jihar Benuwe, Samuel Ortom, a ranar Litinin ya roki ‘yan Najeriya da kada su sanya siyasa a harin da aka kai masa, yana mai cewa hakan ya wuce siyasar bangaranci.

Gwamnan a ranar Asabar ya ce kimanin makiyaya 15, wadanda ke sanye da bakaken kaya, sun bude masa wuta tare da mukarrabansa a gonarsa, inda ya yi ikirarin cewa sai da ya yi tafiyar kimanin kilomita 1.5 don tsiratar da rayuwarsa.

Amma da yake zantawa da manema labarai bayan taron Majalisar Tsaro ta Jiha a New Banquet Hall na gidan Gwamnati, Makurdi, a ranar Litinin, Ortom ya ce ba shi ne gwamna na farko da aka kaiwa hari ba a ‘yan kwanakin nan.

Kada ‘yan Najeriya su sanya siyasa a harin da aka kai mun, in ji Ortom
Kada ‘yan Najeriya su sanya siyasa a harin da aka kai mun, in ji Ortom Hoto: @OrtomSamuel
Source: Twitter

KU KARANTA KUMA: Jami'an Amotekun sun dake makiyaya 9 da shanu 100 a jihar Ondo

Ya ce, “An taba kaiwa gwamnan jihar Borno, wanda yake gwamnan APC ne hari. Ni ne a yau; yana iya zama wani mutum gobe.

“Abin da muke bukata shi ne cewa ya kamata dukkanmu mu hada karfi da karfe don dakatar da wannan saboda kasarmu tana zaune a kan tubalin toka kuma ya kamata mu guji duk wani abin da zai sa ta tarwatse.

"Ko da wannan abu ya faru, akwai wasu Fulani masu kishin kasa da suka kira, saboda haka ya wuce siyasa ta bangaranci saboda duk rayuwar da aka rasa ba za a iya dawo da ita ba."

Yayin da yake yabawa hukuncin da Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda, Mohammed Adamu, ya yi na bincikar lamarin, Ortom ya ce yana jiran gayyatar tawagar masu binciken.

Ya bayyana cewa wannan ba shine karo na farko da kungiyar 'yan asalin Fulani ke yi masa barazana da aiwatar da barazanar ba, jaridar Punch ta ruwaito.

“A shekarar 2018 lokacin da aka kashe mutane 73, FUNAM ta dauki alhakin harin. Lokacin da aka kashe mutane a cikin watan Yuni na wannan shekarar a Filato, FUNAM ta fito ta dau alhaki kuma yanzu sun dauki alhakin.

KU KARANTA KUMA: Najeriya na cikin halin kakanikaye, Ministan Tsaro Bashir Magashi

“Makonni biyu da suka gabata, Miyetti Allah Kataore sun yi wani taro a Yola kuma suka ware ni a matsayin wanda ke haifar da matsala ga kabilar Fulani a Najeriya kuma ba na adawa da kowa. Yawancinsu suna zaune cikin farin ciki a Benue kuma suna gudanar da ayyukansu na halal,” inji Ortom.

A wani labarin, Lawal Musa, shugaban al'ummar Fulani a karamar hukumar Kajuru da ke Kaduna, ya rasa ransa sakamakon wani hari da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka kai, The Cable ta ruwaito.

Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro na cikin gida a Kaduna, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.

Musa, wanda aka fi sani da suna "Alhaji Maijama'a", an ba da rahoton kashe shi a daren Lahadi.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Source: Legit.ng

Online view pixel