Kada ku yarda a kafa dokar halasta sanya Hijabi a makarantu, CAN ga yan majalisa Kiristoci

Kada ku yarda a kafa dokar halasta sanya Hijabi a makarantu, CAN ga yan majalisa Kiristoci

- Kiristoci a Najeriya sun ce ba zasu yarda a halasta sanya Hijabi a Najeriya ba

- Majalisar wakilan tarayya na shirin kafa dokar samar da yancin sanya hijabi a Najeriya

- Kungiyar CAN ta yi kira ga majalisa ta soke wannan doka saboda yana da hadari

Kungiyar Kiristocin Najeriya ta yi kira ga majalisar dokokin tarayya ta dakatad da wani shiri da ake yi a majalisar wakilai na yunkurin halasta amfani da Hijabi a makarantu a fadin tarayya.

A jawabin da Sakatare Janar na kungiyar CAN, Joseph Bade Daramola, ya sake, ya yi gargadin cewa wannan doka bai kamata a wannan lokaci ba, Punch ta ruwaito.

Kungiyar Kiristocin ta kara da cewa halasta sanya Hijabi zai tayar da tarzoma a Najeriya.

Maimakon kokarin kafa doka kan Hijabi, CAN ta bukaci yan majalisun su mayar da hankulansu kan rashin tsaro, rashin aikin yi dss.

A cewar CAN, dokar na kokarin baiwa dalibai mata Musulmai masu son sanya Hijabi daman sanya abinsu ko da a makarantu masu zaman kansu ne.

KU DUBA: Sojoji za su yi luguden wuta na ‘mai uwa da wabe, za a kashe duk wanda ke cikin daji

Kada ku yarda a kafa dokar halasta sanya Hijabi a makarantu, CAN ga yan majalisa Kiristoci
Kada ku yarda a kafa dokar halasta sanya Hijabi a makarantu, CAN ga yan majalisa Kiristoci
Asali: UGC

KU KARANTA: Ganduje: Harin da aka kai wa Gwamnan Benuwai ya kada hanjin sauran Gwamnonin Jihohi

"Maganar gaskiya itace, ba sanya hijabi bane matsalarmu, halasta sanyawa a makarantu masu zaman kansu, musamman makarantun da addininsu ya sabawa Hijabi shine matsala," cewar CAN.

"Halasta sanya Hijabi a makarantu masu zaman kansu zai haifar da rikicin da ba za'a iya dakilewa ba."

"Muna kira ga Kiristoci a dukkan majalisu, har da majalisar dokokin tarayya su tashi tsaye kuma su marawa addininsu baya idan basu yi ridda don siyasa ba."

A wani labarin, shugaban wata ƙungiyar mabiya addinin kirista ta PFN, Bishof Wale Oke, ya gargaɗi gwamnan jihar Kwara, Alhaji Abdul-rahman Abdulrasaq kan kada ya kuskura yafara wani abu da zai iya kai ƙasar nan ga yaƙi, yana mai cewa rikicin hijabi dake faruwa a jihar ka iya zama sababin hakan matuƙar ba'a ɗauki matakin da ya dace ba.

Oke, ya yi wannan jawabi ne a Ibadan ranar Litinin, ya yin da ya karɓi bakuncin mabiyansa daga jihohin Ekiti da Ondo.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Asali: Legit.ng

Online view pixel