Ganduje: Harin da aka kai wa Gwamnan Benuwai ya kada hanjin sauran Gwamnonin Jihohi

Ganduje: Harin da aka kai wa Gwamnan Benuwai ya kada hanjin sauran Gwamnonin Jihohi

- Abdullahi Ganduje ya nuna takaicinsa a kan harin da aka kai wa Samuel Ortom

- Gwamnan Kano ya ce abin damuwa ne ‘Yan bindiga su iya neman ran Gwamna

- Ganduje ya bayyana haka ne yayin da ya gana da ‘Yan jarida a Aso Villa a Abuja

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya bayyana cewa abokan aikinsa sun damu a dalilin harin da aka kai wa takwaransu, Samuel Ortom.

Jaridar This Day ta rahoto Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya na wannan bayani ne a ranar Litinin, 22 ga watan Maris, 2021, a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Mai girma Abdullahi Umar Ganduje ya nuna cewa ya na sa rai kwanan nan za a kawo karshen matsalar rashin tsaron da ake fuskanta a bangarorin Najeriya.

KU KARANTA: Idan wani abu ya faru da ni, a tuhumi Ganduje - Jaafar Jaafar

Gwamna Abdullahi Ganduje ya ce harin da aka kai wa Samuel Ortom na jihar Benuwai abin takaici ne, ya na mamakin yadda za a nemi ran gwamnan jiha.

Dr. Ganduje yake cewa idan za a iya auka wa gwamna, ya talakan da ba kowa ba zai kare a kasar nan.

Gwamnan ya na sa rai sababbin hafsoshin kasar za su kawo gyara ta yadda za a samu tsaro, yayin da su ke kara gane kan aiki bayan an nada su a kwanakin baya.

“Harin abin takaici ne, amma na yi imani tun da an nada sababbin hafsoshin soji, za a kirkiro sababbin dabaru, kuma shugaban kasa da gaske yake yi kan tsaro.”

KU KARANTA: ‘Yan Majalisa su na nemawa tsofaffin Gwamnonin da ke gidan yari afuwar Buhari

Ganduje: Harin da aka kai wa Gwamnan Benuwai ya kada hanjin sauran Gwamnonin Jihohi
Dr. Abdullahi Ganduje Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Gwamnan ya ce: “Amma dai lamarin abin takaici ne.”. Sannan ya bayyana kokarin da yake yi a Kano.

“Ba gwamnoni kurum ake kai wa hari ba, duk wanda aka kai wa hari, ya kamata a damu, rai duk daya ne. Gaskiya mun damu, ya kamata ace gwamna na da tsaro.”

Hakan na zuwa ne bayan gwamnan na Kano ya gana da shugaba Muhammadu Buhari a Aso Villa.

A jiya kun ji cewa Gwamnan jihar Kano ya ziyarci shugaba Muhammadu Buhari domin ya nuna masa hotunan wata katafariyar gada da yake shirin gina wa jama'arsa.

Tuni aka yi wa wannan gada da za ayi a Hotoro suna da shugaban kasar, watau gadar Muhammadu Buhari. Gwamnan ya ce za ayi watanni 18 ne ana aikin

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng