Ba maganar sulhu tsakanin mu da 'yan ta'adda, inji gwamnatin tarayya

Ba maganar sulhu tsakanin mu da 'yan ta'adda, inji gwamnatin tarayya

- Har yanzu ana ganin ko gwamnatin tarayya zata tattauna da 'yan ta'adda ko kuwa baza tayi ba

- Mai bada shawarwari kan harkokin tsaro na ƙasa, Major-General Babagana Monguno ya bayyana tashi matsayar

- Munguno yace babu yadda za'ayi gwamnati ta tsaya tattaunawa da 'yan ta'adda

Mai bada shawara ta musamman kan harkokin tsaro na ƙasar nan, Mejo Janar Babagana Monguno ya ƙara jaddada cewa gwamnatin tarayya bazata tattauna da 'yan bindiga ba.

Mungono yayi wannan jawabi ne ranar Alhamis 11 ga watan maris lokacin da yake zantawa da manema labaran gidan gwmnati a fadar shugaban ƙasa, Villa, babban birnin tarayya, Abuja.

KARANTA ANAN: Da duminsa: Manyan hafsoshin sojojin Nigeria sun dira garin IbadanM

Legit.ng ta bibiyi tattaunawar kai tsaye ta manhajar Youtube.

A cewarsa, yan ta'addan basu da wata hujja na ɗaukar makami sukai hari a wasu kauyuka na yankunan Arewa maso yamma da Arewa maso tsakiya na ƙasar nan.

A bayaninsa yace:

"Su ba mutane ne da suke neman wani abu na gaske Ko na doka ba, Su kawai suna kokarin tada hankula ne ga mutanen da basuji ba basu gani ba. Dole muɗau mataki akansu ta yadda suke so, kuma zamuyi iyakacin kokarin mu mu tabbatar da muradin gwamnati."

"Duk da gwamnati bata ja da tattaunawa da tsirarunsu, Gwamnati zatayi amfani da ƙarfinta gaba ɗaya. Bazai yuwu gwamnati ta tattauna da waɗannan mutanen ba waɗan da basu da tushe kuma zasu cigaba da raunatar da al'umma. Zamuyi amfani da karfin mu wajen maganin waɗannan mutanen."

Ba maganar sulhu tsakanin mu da 'yan ta'adda, inji gwamnatin tarayya
Ba maganar sulhu tsakanin mu da 'yan ta'adda, inji gwamnatin tarayya Hoto: @NGRpresident
Source: Twitter

"Za kuma mu maida hankali akan wasu matakai dake da alaƙa ta kusa da ta'addanci kamar: haramtattun ƙwayoyi, yawaitar ƙananan makamai a cikin jama'a, Haƙar ma'adanai ba bisa ka'ida ba a wurare kamar Zamfara. Wannan na daga cikin abunda ke jawo tashin hankali, kuma mun fara fuskantar su yadda ya kamata."

KARANTA ANAN: Jerin jihohi 16 da suka samu kasonsu na rigakafin COVID-19 da adadin sa suka samu

"A mahangar shugaban ƙasa da kuma umarninsa shine bazamu sa kanmu wajen dogara da wasu ba (sojojin haya) bayan muna da namu mutanen da zasu iya kawar mana da wannan matsalolin. Muna da ma'aikatan mu da kuma kayan aiki, kuma shugaban ƙasa yayi tanadi na musamman ga jamian tsaron mu."

A ranar laraba 3 ga watan maris, wasu haɗakar ƙungiyoyin sakai 15, sun zargi wasu gwamnoni da kokarin maida yawan satar mutane da fashi zuwa harkar samun kuɗi.

Ƙungiyoyin ƙarƙashin jagorancin 'Non-State Actors Consultative Forum (NOSACOF)' sunyi wannan zargin ne a wata zantawa da sukayi a jihar Kano.

A lokacin da yake jawabi a wajen, shugaban haɗakar, Mr Ibrahim Waiya, Yace wasu yan siyasa a arewacin ƙasar nan sun ƙirƙiri wata hanya domin kwashe tattalin arziƙin ƙasa da sunan tattaunawar sulhu da yan ta'adda.

Sannan kuma, ƙungiyoyin da ba na gwamnati ba sun bayyana lamarin a matsayin abun takaici da kuma babban ƙalubale ga demokaraɗiyyar kasar mu, musamman satar ɗalibai mata yan makaranta da akeyi kwanan nan.

A wani labarin kuma Gwamnatin Bayelsa ta kafa dokar hana makiyaya kiwo a faɗin jihar

Ahmad Yusuf dan mutan katsinawa ma'aikacin legit.ng ne a bangaren Hausa. Ya fara aiki da legit kwa nan nan. Ahmad nada burin shahara a aikin jarida.

Kuna iya samunsa a kafar sada zumunta na twitter @ahmadyusufMuha77

Source: Legit

Online view pixel