Gwamnatin Bayelsa ta kafa dokar hana makiyaya kiwo a faɗin jihar

Gwamnatin Bayelsa ta kafa dokar hana makiyaya kiwo a faɗin jihar

- Gwaman jihar Bayelsa, Douye Diri, ya sa hannu a kan dokar hana kiwon dabbobi a jihar

- Ya kuma gargaɗi al'ummar jihar a kan subi dokar sau da kafa don gujewa fushin hukuma

- Kakakin majalisar dokokin jihar ya bayyana cewa an kafa dokar ne don kaucewa faɗa tsakanin manoma da makiyaya.

Gwamnatin jihar Bayelsa ta kafa dokar hana makiyaya kiwo a fili a faɗin jihar.

Gwamnan jihar, Douye Diri, wanda ya amince da dokar kula da kiwo da hada hadar dabbobi ta 2021, a ranar laraban nan data gabata a zaman da aka gudanar a gidan gwamnati, kamar yadda Channels Tv ta ruwaito.

Gwamnan yace dalilin da yasa suka kafa wannan doka shine don tabbatar da zaman lafiya tsakanin masu hada-hadar dabbobi da kuma mazauna jihar.

Sannan kuma dokar zata taimaka wajen kiyaye irin rikice-rikicen da ake samu a sauran sassan ƙasar nan.

KARANTA ANAN: Kwastam sunyi babban kamu, sun kwace kayan 79 miliyan a Kastina

"Gwamnatin Bayelsa na maraba da kowa akan yazo ya nemi abinci cikin zaman lafiya da bin doka. Mutanen Bayelsa nason zaman fahimtar juna tsakanin 'yan jihar dama waɗanda ba 'yan asalin jihar ba," Inji gwamnan.

"Dalilin kafa dokar shine domin a kiyaye rikici daka iya tasowa tsakanin manoma da makiyaya, 'yan jiha da kuma waɗanda ba 'yan asalin jihar ba, kamar yadda yake faruwa a wasu sassa na ƙasar nan," a cewarsa.

Ya kuma ƙara da cewa: "Daga lokacin da aka kafa wannan dokar, ba'a yadda wani mutum ya tara ko yayi kiwo ko kasuwancin dabbobi a faɗin jihar ba face wuraren da wannan kwamitin na kula da dokar ya ware."

Gwamnatin Bayelsa ta kafa dokar hana makiyaya kiwo a faɗin jihar
Gwamnatin Bayelsa ta kafa dokar hana makiyaya kiwo a faɗin jihar Hoto: @Bayelsastategov
Asali: Twitter

Ya kuma ƙara da cewa dokar ta ƙunshi kama duk wani makiyayi da aka gani da makami, ko anyi wa makamin rijista ko ba ayi ba.

Gwamna Diri ya bayyana cewa dokar ta ƙunshi kafa kwamiti dazai kula da dabbobi a jihar.

KARANTA ANAN: Namijin da ba zai iya ba budurwa N300K na kasuwanci ba, bai cancanci a aure shi ba, Uche

Mambobin wannan kwamitin sun haɗa da, kwamishinan noma, hukumomin tsaro, matasa da sauransu.

"Dokar ta hana shigowa da shanu da kafa daga wasu sassan ƙasar nan zuwa jihar Bayelsa, kafin ka shigo da dabbobin sai likitocin fannin sun duba sun baka izini da dai sauransu," Inji gwamnan.

Diri yace, daga sanda aka amince da dokar, duk mutumin da aka gani yana yawo da dabbobi a kafafuwan su za'a kamashi da laifin karya doka.

Gwamnan ya kuma ƙara amincewa da wata doka da zata hana cutar da mata da ƙananan yara a faɗin jihar.

A nasa jawabin, Kakakin majalisar dokokin jihar, Rt Hon Abraham Ingobere, ya bayyana cewa anyi dokar ne don kaucewa matsalolin rashin jituwa tsakanin manoma da makiyaya.

A wani labarin kuma Sabon shugaban EFCC ya shiga aiki, ya ce an fara karbo kudin cuwa-cuwar tallafin fetur

Abdulrasheed Bawa ya ce Hukumar EFCC ta sha alwashin kai barayin gidan yari

Kawo yanzu EFCC ta iya karbo N20bn daga cikin N70bn da aka gano an wawura

Ahmad Yusuf dan mutan katsinawa ma'aikacin legit.ng ne a bangaren Hausa. Ya fara aiki da legit kwa nan nan. Ahmad nada burin shahara a aikin jarida.

Kuna iya samunsa a kafar sada zumunta na twitter @ahmadyusufMuha77

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel