Da duminsa: Manyan hafsoshin sojojin Nigeria sun dira garin Ibadan

Da duminsa: Manyan hafsoshin sojojin Nigeria sun dira garin Ibadan

- Sabbin hafsoshin sojojin Nigeria sun tafi garin Ibadan, babban birnin jihar Oyo

- Shugabannin sojojin sun isa garin ne a yau Alhamis don gana wa da Gwamna Makinde kan wasu batutuwan tsaro da suka taso a jihar

- Yayin ziyarar, shugabannin sojojin za su sa ido kan sauyin shugabannin sojoji da za a yi a jihar Oyo

Manyan hafsoshin sojojin Nigeria sun isa garin Ibadan, babban birnin jihar Oyo, rahoton The Nation.

Karkashin jagorancin babban hafsan tsaro, Janar Leo Irhabor, sun isa 2 Division ta Rundunar Sojojin Nigeria inda Janar Irhabor zai yi wa jami'ai da sojojin Nigeria a Ibadan jawabi.

DUBA WANNAN: Bayan haihuwar yara 5, matar manomi ta sake haifar masa ƴan biyar

Da duminsa: Manyan hafsoshin sojojin Nigeria sun dira garin Ibadan
Da duminsa: Manyan hafsoshin sojojin Nigeria sun dira garin Ibadan. Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

Za su gana da Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo kuma su sa ido kan yadda za a yi canjin shugabannin sojoji a sansanin sojojin da ke Ibadan.

Babban sakataren watsa labarai na gwamnan, Mr Taiwo Adisa ya tabbatar wa wakilin The Punch hakan.

KU KARANTA: N2.5bn: Ban taɓa damfarar gwamnatin tarayya ba, in ji Zahra Buhari

Ya ce, "Eh, sun iso Ibadan. Sun kusa zuwa domin ganawa da gwamna."

Akwai wasu matsalolin tsaro da suka taso a jihar Oyo don haka ana sa ran za a tattauna yadda za a magance matsalolin a wurin taron.

A wani rahoton daban kun ji cewa, rundunar yan sandan jihar Kano ta kwantar da jama'a hankula game da wasu bakin mutane tare da rakuma da suka bayyana a wasu sassan jihar.

Daily Nigerian ta gano cewa mazauna jihar sun ankarar da yan sanda kan bakin mutanen da suka yada zango a wasu sassan jihar.

Wasu mazauna garin suna zargin matafiyar sun iso jihar ne domin aikata laifi da sunan fataucin kanwa.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164