Jerin jihohi 16 da suka samu kasonsu na rigakafin COVID-19 da adadin da suka samu
Jihohi daban-daban a fadin tarayya sun kaddamar da yiwa al'ummarsu rigakafin cutar Korona.
Kawo yanzu, jihohi 16 cikin 36 na kasar sun samu nasu kason na rigakafi daga gwamnatin tarayya.
A cewar jaridar Leadership, jihohi 16 sun karbi jimillan rigakafin Oxford-AstraZeneca 1,871,050.
DUBA NAN: Gwamnatin Bayelsa ta kafa dokar hana makiyaya kiwo a faɗin jihar
Ga jerin jihohin da suka samu rigakafin da adadin da suka samu:
1. Jihar Benue - 78,108,
2. Jihar Borno - 75,510
3. Jihar Ekiti - 52,000
4. Jihar Jigawa - 68,000
5. Jihar Nasarawa - 61,000
6. Jihar Niger - 74,110
7. Jihar Ondo - 73, 570
8. Jihar Cross River - 50,840
9. Jihar Osun - 64,240
10. Jihar Ebonyi - 42,090
11. Jihar Plateau - 105,600
12. Jihar Ogun - 100,000
13. Jihar Adamawa - 59,280
14. Jihar Lagos - 507,000
15. Jihar Kano - 200,000
16. Jihar Kaduna - 180,000
KU KARANTA: Gwamnan Neja ya bada umurnin rufe dukkan makarantun sakandaren gwamnatin jihar
Gabanin yanzu, gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya ce sam shi ba zai karbi rigakafin COVID-19 ba saboda ba ya bukata.
Ya bayyana cewa shi bai da wata matsalar lafiya da ke bukatar ya yi rigakafin.
Kun ji cewa gwamnatin jihar Kano ta samu karban rigakafin AstraZeneca na cutar Korona.
Kwamishanan kiwon lafiya na jihar, Aminu Tsanyawa, ne ya karbi rigakafin ranar Talata a tashar jirgin Malam Aminu Kano madadin gwamnan jihar.
Tsanyawa ya ce gwamnatin jihar za ta fara mayar da hankali da jami'an kiwon lafiya wajen basu rigakafin kafin yiwa gamagarin jama'a.
Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.
Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.
Asali: Legit.ng