Kungiyar Arewa ga gwamnan Neja: Ka farka sannan ka tsare mutanen ka daga 'yan fashi

Kungiyar Arewa ga gwamnan Neja: Ka farka sannan ka tsare mutanen ka daga 'yan fashi

- An karfafawa gwamnan jihar Neja gwiwa don dakile matsalar rashin tsaro da ke kara ta'azzara a jihar

- Kungiyar Arewa Citizens Against Insecurity (ACAI) ta yi kira ga gwamnan da 'yan majalisar jihar da su farka daga bacci su fuskanci abubuwan da ke faruwa

- A cewar matasan, aiki tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari na iya taimakawa wajen kawo karshen yan bindiga a jihar

Matasa a karkashin kungiyar Arewa Citizens Against Insecurity (ACAI) a ranar Juma’a, 19 ga watan Fabrairu, sun yi kira ga gwamnan jihar Neja, Sani Bello, da ya yi kokarin shawo kan matsalar rashin tsaro a jihar.

Wannan kiran ya biyo bayan sace daliban makarantar Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati da ke Kagara da wasu a jihar.

KU KARANTA KUMA: Gwamnan Zamfara ya yi amai ya lashe bayan ya ce ba duka yan bindiga bane na banza

Kungiyar Arewa ga gwamnan Neja: Ka farka sannan ka tsare mutanen ka daga 'yan fashi
Kungiyar Arewa ga gwamnan Neja: Ka farka sannan ka tsare mutanen ka daga 'yan fashi Hoto: @abusbello
Source: Twitter

A wata sanarwa dauke da sa hannun sakatare-janar na ACAI, Hosea Adamu, wanda Legit.ng ta gani, kungiyar ta ce akwai bukatar gwamnan da ‘yan majalisar daga jihar su farka don fuskantar abubuwan da ke faruwa.

Da yake nuna damuwar sa game da batun daurawa juna laifi da ke faruwa tsakanin gwamnan da 'yan majalisar daga jihar, Adamu ya ce ya kamata a dauki kwararan matakai don kawo karshen ayyukan' yan fashi a Neja.

Ya kuma shawarci gwamna, sanatoci, da sauran ‘yan majalisa a jihar da kuma masu rike da mukaman siyasa da su hada kai da Shugaba Muhammadu Buhari don maido da zaman lafiya da tsaro a Neja.

Adamu ya ce yana da matukar mahimmanci gwamnati ta saka jari wajen fadakar da shugabannin addinai da na gargajiya a jihar don yin garambawul kan bukatar su hana mabiyansu shiga wannan mummunan aiki na ta’addanci.

Ya bukaci gwamnan da sauran shugabanni a jihar da su yi aiki cikin sauri maimakon cika jama'a da maganganu marasa ma’ana.

KU KARANTA KUMA: Tsohon Shugaban tsaro ya bayyana inda yakin Najeriya na gaba zai gudana

A gefe guda Sakataren gwamnatin jihar Neja, Ahmed Ibrahim Matane ya yi kira ga 'yan bindiga da su rungumi tattaunawa, sulhu sannan kuma su ajiye makamansu.

Sakataren jihar wanda ya raka malamin addinin Musulunci da ke Kaduna, Sheikh Ahmed Abubakar Gumi don ganawa da 'yan fashin ya bayyana cewa gwamnati a shirye take ta tattauna da su.

Kamar dai yadda 'yan fashin suka ba da sharadin zama lafiya a jihar sun ce akwai bukatar gwamnati ta saki mutanensu da ke hannun jami'an tsaro.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Source: Legit.ng

Online view pixel