Tsohon Shugaban tsaro ya bayyana inda yakin Najeriya na gaba zai gudana

Tsohon Shugaban tsaro ya bayyana inda yakin Najeriya na gaba zai gudana

- Tsohon Shugaban ma’aikatan tsaro, Abayomi Olonisakin ya bayyana inda yakin Najeriya na gaba zai barke

- Olonisakin ya ce a bisa ga binciken da yayi shekaru uku da suka gaba, ya gano cewa Najeriya na da gandun daji sama da dubu wanda ya zama mafakar miyagun mutane

- Ya fadi hakan ne a yayin tantance shi da majalisar dokoki tayi don samun mukamin jakadanci

Tsohon Shugaban ma’aikatan tsaro, Abayomi Olonisakin, a ranar Alhamis, 18 ga watan Fabrairu ya bayyana cewa yaki da rikice-rikicen Najeriya na gaba zai kasance a cikin dazuzzuka.

Janar din sojan mai ritaya, wanda ya yi murabus a matsayin babban Shugaban ma’aikatan tsaro a watan Janairun da ya gabata bayan shafe shekaru shida yana aiki a babban mukamin, ya yi wannan bayanin ne yayin da ake tantance shi a Majalisar Dokokin Tarayya.

Majalisar na tantance shi sakamakon aika sunansa da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi zauren don nada shi mukamin jakadanci.

Tsohon Shugaban tsaro ya bayyana inda yakin Najeriya na gaba zai gudana
Tsohon Shugaban tsaro ya bayyana inda yakin Najeriya na gaba zai gudana Hoto: @ekitistategov
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: 2023: Tsohon gwamna ya bude wani babban sirri, ya ce nan ba da dadewa ba Wike zai koma APC

A cewar Olonisakin, wani bincike da ya gudanar a kan dazuzzuka shekaru uku da suka gabata ya nuna cewa Najeriya tana da gandun daji sama da dubu kuma akwai matukar bukatar mutum da kare gandun dajin wadanda suka zama maboyar masu aikata laifi.

A bisa ga rahoton Bankin Duniya na 1992, gandun dajin Najeriya ya kai kashi 10 cikin dari na duk fadin kasar, Channels TV ta ruwaito.

Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, a watan Janairun da ya gabata ya umarci masu zama a dajin jihar ba bisa ka’ida ba da su bar gandun dajin, lamarin da ya haifar da cece-kuce.

KU KARANTA KUMA: Sheikh Gumi: Za a sako waɗanda aka sace a GSC Kagara nan ba da daɗewa ba

A wani labarin, Auwal Daudawa, wanda ya jagoranci sace daliban Makarantar Sakandaren Kimiyya ta Gwamnati, Kankara, Jihar Katsina, ya ce ya jagoranci wannan samamen ne saboda Gwamna Bello Masari ya kuskurewa dakarunsa.

A wata tattaunawa ta musamman da ya yi da jaridar Daily Trust, Daudawa ya ce ya so tabbatar wa da gwamnati cewa yana da karfin da zai kai irin wannan harin.

Ya ce Masari ya saba zabin tattaunawa da kungiyarsa kuma ya so ya nuna wa gwamnan cewa za su iya haddasa tashin hankali.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng