Yanzu Yanzu: SSG na Neja ya jagoranci tawaga don ganawa da 'yan bindiga

Yanzu Yanzu: SSG na Neja ya jagoranci tawaga don ganawa da 'yan bindiga

- SSG na jihar Neja, Ahmed Ibrahim Matane ya jagoranci tawaga don ganawa da 'yan bindiga

- Matani ya bukaci yan ta'addan da su rungumi shirin yin sulhu domin samun maslaha ga lamarin rashin tsaro da ke addabar jihar

- Ya kuma nemi su ba gwamnati hadin kai a kokari da take yi don ceto matafiya da daliban makarantar Kagara da aka yi garkuwa da su a jihar

Sakataren gwamnatin jihar Neja, Ahmed Ibrahim Matane ya yi kira ga 'yan bindiga da su rungumi tattaunawa, sulhu sannan kuma su ajiye makamansu.

Sakataren jihar wanda ya raka malamin addinin Musulunci da ke Kaduna, Sheikh Ahmed Abubakar Gumi don ganawa da 'yan fashin ya bayyana cewa gwamnati a shirye take ta tattauna da su.

Kamar dai yadda 'yan fashin suka ba da sharadin zama lafiya a jihar sun ce akwai bukatar gwamnati ta saki mutanensu da ke hannun jami'an tsaro.

Yanzu Yanzu: SSG na Neja ya jagoranci tawaga don ganawa da 'yan bindiga
Yanzu Yanzu: SSG na Neja ya jagoranci tawaga don ganawa da 'yan bindiga Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: Gwamnan Zamfara ya yi amai ya lashe bayan ya ce ba duka yan bindiga bane na banza

Matane ya yi jawabi ga ‘yan fashin da kwamandojinsu a Dutsen Magaji, karamar hukumar Mariga ta jihar Neja inda ya bukace su da su rungumi tattaunawar zaman lafiya da gwamnati ta fara.

Ya bayyana cewa tattaunawar zaman lafiyar za ta kawo karshen matsalolin tsaro da jihar ke fuskanta, jaridar The Nation ta ruwaito.

Matane ya kara yin kira ga Kwamandojin ‘yan fashin da su goyi bayan kokarin da gwamnati ke yi na ganin an saki fasinjojin da suka sace na Hukumar Kula da Sufuri ta Jihar Neja da Daliban Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati, Kagara.

Ya ce za a shigo da shugabannin addinai da sauran masu ruwa da tsaki cikin tattaunawar da ake yi da ‘yan fashi, masu satar mutane, da barayin shanu a shirin samar da zaman lafiya da gwamnati ta fara.

A gefe guda, mun ji cewa Shahararren malamin addinin Islama, Sheikh Gumi, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta ba 'yan fashi da ke son yin sulhu idan har za a magance matsalar tsaro a yanzu.

KU KARANTA KUMA: Tsohon Shugaban tsaro ya bayyana inda yakin Najeriya na gaba zai gudana

Malamin ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a yayin ganawa da manema labarai a Minna, babban birnin jihar Neja.

Wannan ya faru ne bayan malamin ya ziyarci sansanin wasu yan fashi da ke aiki a jihar Neja.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel