Gwamnan Zamfara ya yi amai ya lashe bayan ya ce ba duka yan bindiga bane na banza

Gwamnan Zamfara ya yi amai ya lashe bayan ya ce ba duka yan bindiga bane na banza

- Gwamna Matawalle ya yi martani kan wata magana mai cike da rudani da yayi game da 'yan fashi

- Gwamnan na Zamfara ya ce kuskuren harshe yayi a maganar tasa

- Matawalle ya sha suka saboda cewa da yayi ba duka yan fashin bane masu laifi

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Mohammed, ya yi karin haske kan wata sanarwa da ya yi yayin ziyarar da ya kaiwa Shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Gwamnan ya je fadar Shugaban kasar domin yi masa bayani game da yanayin tsaro a jihar.

Yayin da yake zantawa da manema labarai bayan ziyarar, Mohammed ya ce ba duk ‘yan fashi da ke aiki a jihar ne na banza ba.

Gwamnan Zamfara ya yi amai ya lashe bayan ya ce ba duka yan bindiga bane na banza
Gwamnan Zamfara ya yi amai ya lashe bayan ya ce ba duka yan bindiga bane na banza Hoto: @Zamfara_state
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Tsohon Shugaban tsaro ya bayyana inda yakin Najeriya na gaba zai gudana

Ya yi bayanin cewa yawancin 'yan fashin suna daukar makami ne saboda rashin adalci da wasu daga cikin al'umma ke musu.

Wannan furuci nasa ya janyo masa shan suka bayan kafofin watsa labarai sun wallafa shi.

Amma a wata sanarwa a ranar Alhamis, gwamnan ya ce yana nufin ya ce ba duka Fulani ne masu laifi ba, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Sanarwar wanda mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Zailani Bappa ya sanya wa hannu, ta ce gwamnan ba yana nufin ya ce ba dukkan 'yan fashi ne masu laifi ba.

Sanarwar ta ce:

"Wani labari da kafar yada labarai ta yanar gizo, Premium Times ta dauka a yau, ya ambato Gwamna Bello Mohammed (Matawallen Maradun) yana cewa ba duk 'yan fashi bane masu laifi.

"Tabbas, mai girma gwamna ya kasance a fadar shugaban kasa a jiya don yi wa shugaban kasar bayanin halin tsaro a jihar. Ya kuma bayar da damar yin gajeriyar hira da 'yan jaridar a villa.

"A waccan hirar, ya yi ƙoƙari ya bayyana sanannen ra'ayinsa cewa ba duk FULANI ne masu laifi ba. Ya ci gaba da bayanin rashin adalci da aka yi musu kamar sace shanunsu a matsayin dalilan da suka ingiza su zuwa aikata laifuka.

KU KARANTA KUMA: 2023: Tsohon gwamna ya bude wani babban sirri, ya ce nan ba da dadewa ba Wike zai koma APC

"Idan da gaske ya ambaci kalmar Yan fashi maimakon FULANI, to bisa kuskure ne.

"Muna son yin kira ga duk 'yan Najeriya da suka ci karo da wannan labarin da su yi watsi da sakon saboda sam wannan ba abin da mai girma gwamna yake nufi ne ba ne ko kuma irin sakon da yake son bayyanawa."

A baya mun ji cewa Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya ce ba duka tsagerun yan bindiga bane mutanen banza, wasu kawai dole ce ta wajabta musu daukar bindiga.

Gwamnan ya bayyana hakan ne ga manema labarai bayan ganawa da shugaba Buhari a fadar shugaban kasa ranar Alhamis, 18 ga Febrairu, 2021, Vanguard ta ruwaito.

Ya yi bayanin cewa yawancin yan bindigan sun shiga harkar ne saboda irin rashin adalcin da al'ummar gari ke musu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel