An rufe majalisar Ghana bayan mambobi da ma'aikata 168 sun harbu da korona

An rufe majalisar Ghana bayan mambobi da ma'aikata 168 sun harbu da korona

- An rufe majalisar dokokin kasa ta Ghana saboda yaduwar annobar korona

- A halin yanzu yan majalisa da ma'aikata guda 168 ne suka harbu da mugunyar cutar

- Kakakin majalisar ya ce yaduwar cutar ya saka dole za su rufe na sati uku don a yi feshin magani

Kasar Ghana ta rufe majalisar dokokin kasar na tsawon makonni uku saboda karuwar yaduwar cutar korona a tsakanin mambobin majalisar da wasu ma'aikata.

A kalla yan majalisa 17 da ma'aikatar majalisar 151 ne suke dauke da kwayar cutar a halin yanzu, The Cable ta ruwaito.

An rufe majalisar Ghana bayan mambobi da ma'aikata 168 sun harbu da korona
An rufe majalisar Ghana bayan mambobi da ma'aikata 168 sun harbu da korona. Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

Karuwar yaduwar cutar ya tilastawa majalisar takaita ranakun zamanta zuwa Talata da Alhamis inda mambobi da ma'aikatan da ake bukata kawai ke shiga.

DUBA WANNAN: Ku binciko bata-garin da ke cikin ku, Obaseki ya faɗawa makiyaya

Alban Bagbin, kakakin majalisar wanda ya sanar da rufewar a ranar Talata, ya ce majalisar za ta tafi hutu a ranar 2 ga watan Maris domin 'feshin magani a harabar majalisar'.

"Ni da shugabannin majalisar sun tattauna mun yanke shawarar dage zaman majalisar na tsawon makonni uku," in ji Bagbin.

Bagbin ya ce kwamitocin majalisar za su cigaba da zama domin nazari kan wadanda Shugaba Nana Akufo-Addo ya tura sunanyensu a matsayin ministoci.

KU KARANTA: Tsohon mai tsaron baya na Super Eagles, Sofoluwe, ya riga mu gidan gaskiya

A ranar Litinin da ta gabata, Kungiyar Likitoci na Ghana, GMA, ta ce likitoci bakwai sun mutu sakamakon kamuwa da cutar ta korona a kasar.

Kasar ta ruwaito cewa mutane 73,003 ne suka kamu da cutar tun farkon bullarta inda mutum 482 suka mutu.

A wani labarin daban, Rundunar Sojojin Nigeria ta nada Mohammed Yerima a matsayin sabon direktan sashin hulda da jama'a, The Cable ta ruwaito.

Yerima, mai mukamin Brigedier-Janar zai maye gurbin Sagir Musa wanda ya kasance kakakin sojin na rikon kwarya tun shekarar 2019.

Kafin nadinsa, Yerima ya rike mukamin direktan sadarwa na tsaro da kuma mataimakin direkta a hedkwatar tsaro.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel