Turkmenistan: Shugaban ƙasa ya naɗa ɗansa a matsayin 'mataimakinsa'

Turkmenistan: Shugaban ƙasa ya naɗa ɗansa a matsayin 'mataimakinsa'

- Shugaban Turkmenistani, Gurbanguly Berdymukhamedov ya nada dansa a matsayin mataimakin shugaban gwamnati

- Shugaba Berdymukhamedov ya yi amfani da karfin ikonsa a doka ya kirkiri sabuwa ofishin kamar yadda wata jaridar kasar ta ruwaito

- Ana tsammanin dansan, Serdar Berdymukhammedov, mai shekaru 39 shine zai maye gurbin mahaifinsa mai shekaru 63 da a yanzu ya yi shekaru 14 a mulki

Gurbanguly Berdymukhamedov, shugaban kasar Turkmenistani ya kirkiri sabon mukami na mataimakin shugaban gwamnati ya nada dansa a cikin wata doka da aka wallafa a jaridar Neutralny Turkmenistan a ranar Juma'a.

Ana yi wa Serdar Berdymukhammedov, mai shekaru 39 kallon wanda zai gaji mahaifinsa mai shekaru 63 a duniya.

Turkmenistan: Shugaban ƙasa ya naɗa ɗansa a matsayin 'mataimakinsa'
Turkmenistan: Shugaban ƙasa ya naɗa ɗansa a matsayin 'mataimakinsa'. Hoto: @daily_nigerian
Asali: Twitter

Aikinsa shine zamanantar da tsare-tsaren kasar da kuma inganta harkokin mulki.

Shine kuma zai kasance mai kula da harkokin zamani na kasar mai arzikin man fetur.

DUBA WANNAN: Bidiyon rikicin da aka yi tsakanin Hausawa da Yarbawa a Ibadan

Gurbanguly Berdymukhamedov wanda ya shafe shekaru 14 a kan karagar mulki shugaba ne da ake yi wa kallon yana tsaurarawa wurin mulkar kasar.

A hukumance, babu ko mutum daya da ya kamu da cutar korona a kasar ta Turkmenistan duk da yadda annobar ta yi barna sosai a yankin.

Ana kuma sukar Berdymukhamedov saboda irin tsangwama da wasu tsauraran matakai da yake dauka kan wadanda ke sukar gwamnati ko rashin goyon bayansa.

KU KARANTA: Ana iya amfani da NIN don gano ɓata-garin makiyaya, in ji Ganduje

Har wa yau ana sukar yadda ya ke son kashe kudade a kan abubuwa masu tsada na alatu ko na neman suna.

A wani labarin daban, Rundunar Sojojin Nigeria ta nada Mohammed Yerima a matsayin sabon direktan sashin hulda da jama'a, The Cable ta ruwaito.

Yerima, mai mukamin Brigedier-Janar zai maye gurbin Sagir Musa wanda ya kasance kakakin sojin na rikon kwarya tun shekarar 2019.

Kafin nadinsa, Yerima ya rike mukamin direktan sadarwa na tsaro da kuma mataimakin direkta a hedkwatar tsaro.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Asali: Legit.ng

Online view pixel