Babu wanda ya isa ya kore mu daga yankin kudu maso yamma, in ji Miyetti Allah

Babu wanda ya isa ya kore mu daga yankin kudu maso yamma, in ji Miyetti Allah

- Kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah ta ce makiyaya da ba zu bar yankin kudu maso yamma na Nigeria ba

- Sakataren kungiyar na kasa, Alhassan Saleh ya ce kundin tsarin mulki ya basu zabin zama a duk yankin da suke so

- Saleh ya kuma ce aikin hukumomin tsaro ne su binciko masu laifi da gurfanar da su a maimakon tsangwamar kabila baki daya

Kungiyar makiyaya Fulani na MIyetti Allah Kautal Horre ta sha alwashin cewa ba za ta bar yankin kudu maso yammacin kasar ba duba da cewa kundin tsarin mulkin Nigeria ya bawa kowa damar zama duk inda ya ke so.

Miyetti Allah ta kuma sha alwashin rama dukkan hare-haren da ake zargin an kaiwa mambobinta da shanunsu, inda ta ce ba za ta amince da rashin adalcin da ake yi wa makiyaya ba.

Babu wanda ya isa ya kore mu daga yankin kudu maso yamma, in ji Miyetti Allah
Babu wanda ya isa ya kore mu daga yankin kudu maso yamma, in ji Miyetti Allah. Hoto: @MobilePunch
Asali: Facebook

Sakataren kungiyar na kasa, Alhassan Saleh ne ya yi wannan furucin a hirar da Sunday Punch ta yi da shi akan wa'adin ficewa barin kudancin kasar da kungiyoyi da mutanen kudu maso yamma suka bawa makiyaya.

KU KARANTA: 'Yan bindiga mutane ne masu kunya, in ji Sheikh Ahmad Gumi

Saleh ya ce ba daidai bane a kori makiyaya daga kowanne bangare na Nigeria kuma idan akwai bata gari cikinsu, aikin gwamnati ne da jami'an tsaro su binciko su su hukunta su.

Ya ce korar makiyaya daga kudancin kasar abu ne da ba zai haifar da da mai ido ba kuma hanyar da ta dace a bi don maganin rikicin makiyaya da manoma shine gwamnatocin jihohi su samarwa makiyaya wuraren kiwo tare da fitar musu da burtali.

A watan Janairu, gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu ya umurci makiyaya da ke dazukan jiharsa su fice daga bisani ya basu wa'adin kwanaki bakwai.

Ya bada umurnin ne yayin taro da shugabannin hausa Fulani da Ebira a jihar inda ya ce abubuwan da makiyaya ke yi na kawo barazanar tsaro a jihar.

DUBA WANNAN: Turkmenistan: Shugaban ƙasa ya naɗa ɗansa a matsayin 'mataimakinsa'

Daga baya wasu kungiyoyin da mutane a wasu jihohin Yarabawa sun bi sahun jihar Ondo na neman makiyaya su fice daga jihohinsu, a wasu wuraren kuma har da kai musu hari.

A wani labarin daban, Rundunar Sojojin Nigeria ta nada Mohammed Yerima a matsayin sabon direktan sashin hulda da jama'a, The Cable ta ruwaito.

Yerima, mai mukamin Brigedier-Janar zai maye gurbin Sagir Musa wanda ya kasance kakakin sojin na rikon kwarya tun shekarar 2019.

Kafin nadinsa, Yerima ya rike mukamin direktan sadarwa na tsaro da kuma mataimakin direkta a hedkwatar tsaro.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164