Sojojin saman Najeriya sun yi luguden wuta a kan yan bindiga a dajin Kaduna

Sojojin saman Najeriya sun yi luguden wuta a kan yan bindiga a dajin Kaduna

- Dakarun sojin sama sun ragargaji 'yan bindiga a dajin jihar Kaduna

- Sojin sun yi ruwan wuta kan ‘yan fashi a garuruwan da suka hada da Rahama, Tami, Sabon Birni, Galadimawa, Ungwan Farinbatu, Sabuwa, Kutemeshi, Gajere, Sabon Kuyello da sauransu

- Sun kuma yi nasarar halaka yan bindiga da dama da ke kokarin tserewa da dabbobi

An kashe 'yan bindiga da dama yayin da jiragen sama ke gudanar da aikin leken asiri a wurare a jihar Kaduna.

Jiragen saman rundunar sun ragargaji ‘yan fashi a garuruwan Rahama, Tami, Sabon Birni, Galadimawa, Ungwan Farinbatu, Sabuwa, Kutemeshi, Gajere, Sabon Kuyello, Dogon Dawa, Ngade Allah, Kidandan, da kuma yankunan da ke kusa da karamar hukumar Birnin Gwari da Giwa.

Samuel Aruwan, Kwamishinan ma’aikatar tsaron cikin gida na jihar Kaduna, ya bayyana a ranar Laraba, cewa bayanan aikin da aka gabatarwa Gwamnatin Jihar ya nuna cewa duk da cewar an gudanar da cikakken bincike a kan yankin baki daya, ba a ga wani abu ba.

Sojojin saman Najeriya sun yi luguden wuta a kan yan bindiga a dajin Kaduna
Sojojin saman Najeriya sun yi luguden wuta a kan yan bindiga a dajin Kaduna Hoto: Punchng.com
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: An damke wani mutum da ya shirya sace matarsa don yin kudi da ita

Tawagar sun ci gaba da gudanar da aiyuka a Sabon Madada, Babban Doka, Gwaska, Gajere, da kuma garuruwan da ke kusa da su.

A Sabon Madada, an ga 'yan fashi tare da shanu da yawa suna gudu daga garin a hanyar zuwa gabashin wurin. Nan take aka fafata da su sannan aka kashe su.

Sauran wuraren sun bayyana cikin kwanciyar hankali ba tare da fuskantar wata barazanar ba Vanguard ta ruwaito.

Gwamna Nasir El-Rufai ya godewa matukan jirgin saboda aikin da suka yi ya kuma ya yaba da kokarinsu a yankunan. Za a ci gaba da aikin sintiri ta sama a yankin gaba ɗaya.

KU KARANTA KUMA: Wuta ta lakume sabuwar motar wata budurwa kirar Mercedes-Benz yan awanni bayan ta nuna wa duniya ita

A wani labari na daban, ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mataimaki na musamman ga Mataimakin Gwamnan Taraba, Alhaji Bala Baba.

Wata majiya daga danginsa ta shaida wa jaridar The Nation cewa an sace Bala ne a gidansa da ke yankin Sabongari na Jalingo da misalin karfe 1.30 na safiyar ranar Talata, 9 ga watan Fabrairu.

A cewar majiyar, 'yan bindigar sun mamaye yankin, inda suka yi ta harbi ba kakkauta na sama da mintuna 30 kafin suka tafi da shi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel