Yanzu Yanzu: 'Yan bindiga sun sace hadimin mataimakin gwamnan Taraba
- Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da hadimin mataimakin gwamnan jihar Taraba
- Yan bindigar sun sace Bala Baba ne daga gidansa da ke yankin Sabongari a Jalingo a ranar Talata, 9 ga watan Fabrairu
- Rundunar yan sandan ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta ce ta fara bincike don gano masu laifin
‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mataimaki na musamman ga Mataimakin Gwamnan Taraba, Alhaji Bala Baba.
Wata majiya daga danginsa ta shaida wa jaridar The Nation cewa an sace Bala ne a gidansa da ke yankin Sabongari na Jalingo da misalin karfe 1.30 na safiyar ranar Talata, 9 ga watan Fabrairu.
A cewar majiyar, 'yan bindigar sun mamaye yankin, inda suka yi ta harbi ba kakkauta na sama da mintuna 30 kafin suka tafi da shi.
KU KARANTA KUMA: Dalilin da ya sa Shugaba Buhari ba zai taba barin Fani-Kayode ya koma APC ba, jigon jam’iyya
Majiyar ta ci gaba da bayyana cewa bayan sace shi, ‘yan bindigar sun ja Baba inda suka nufi yankin Gongon -Malik da ke Jalingo.
Ya ce har yanzu masu garkuwan ba su fara tattaunawa da yan uwansa ba.
Lokacin da aka tuntube shi, mukaddashin jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan Taraba, ASP Reform Leha, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce bincike ya kankama tare da nufin damko masu laifin.
KU KARANTA KUMA: Tirkashi: 'Yan daba sun sake tarwatsa wani taron APC a Kwara, sun lalata motoci
A wani labarin, mun ji cewa mazauna yankin Randagi da ke karamar Hukumar Birnin Gwari a Jihar Kaduna suna tserewa daga gidajensu kwanaki kadan bayan da ‘yan bindiga suka far wa yankin.
Wadanda suka gudu, galibinsu mata, yara, tsofaffi sun tattara kayansu a ranar 6,7 da 8 ga watan Fabrairu don neman mafaka tare da danginsu a garin Birnin Gwari da makwabtan jihar Neja.
Daily Trust ta ruwaito yadda barayin suka mamaye kauyen wanda ya sa maza suka kori matansu daga garin.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng