Wuta ta lakume sabuwar motar wata budurwa kirar Mercedes-Benz yan awanni bayan ta nuna wa duniya ita

Wuta ta lakume sabuwar motar wata budurwa kirar Mercedes-Benz yan awanni bayan ta nuna wa duniya ita

- 'Yan awanni bayan nuna wa duniya motarta kirar Mercedes-Benz, wata mata' yar Najeriya ta rasa motar alfarmar a wata gobara

- Bidiyon yadda lamarin ya faru ya bayyana a shafukan sada zumunta kuma wasu 'yan Najeriya sun yi gargadi a kan bayyana nasarorin da mutum ya samu a yanar gizo

- Lokacin da aka sayi motar, matar ta yi bidiyo na ciki da wajenta don bayyana irin farin cikin da ta riski kanta a ciki sakamakon mallakar sabuwar abar hawan

- Wasu daga cikin wadanda suka bayyana ra'ayoyinsu game da bidiyon da ya karade shafukan sada zumunta sun danganta lamarin ga makiya masu hana ruwa gudu

Wata matashiya 'yar Najeriya ta yi asarar motar ta kirar Mercedes-Benz ta naira miliyan 9 sakamakon konewa da tayi yan awanni kadan bayan ta haska motar a shafukan sada zumunta.

A cikin wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta, an gano matar a cikin motar ta na nuna farin ciki bayan ta sayi sabuwar abar hawan.

KU KARANTA KUMA: Rikicin makiyaya: Buhari ba mai yawan magana bane, ba zai iya magana a kan komai ba, fadar shugaban kasa

Wuta ta lakume sabuwar motarta kirar Mercedes-Benz yan awanni bayan ta nuna wa duniya ita
Wuta ta lakume sabuwar motarta kirar Mercedes-Benz yan awanni bayan ta nuna wa duniya ita Hoto: Maciej Luczniewski/NurPhoto
Asali: Getty Images

Sai dai kuma, motar ta kone kurmus yan sa’o’i bayan matar ta wallafa ta a shafin soshiyal midiya, lamarin da ya sa yan Najeriya tofa albarkacin bakunansu.

@horlar_aushbiggie ya wallafa:

“Abunda soshiyal midiya zai ja ma wasu mutane ko sannu nan gaba ki wallafa a Facebook babu wanda ya damu da farin cikinki kawai ki yi shi a saukake."

@moses_ashadu ya yi martani:

“Na ga wannan motar a ranar da abun ya faru, abun bakin ciki shine wutar ta fara ci a kusa da wani gidan mai amma suka ki taimakawa da abun kashe goabara.”

@iambalekzypharah ya rubuta:

“Benz na da matsalar lantarki da yawa.”

KU KARANTA KUMA: Ina nan da raina ban mutu ba – Tsohon kwamishinan yan sandan Kano, CP Muhammad Wakili

A gefe guda, gaskiya ne maganar da ke cewa akwai iyawa cikin nakasa. Wani saurayi ya jajirce ba tare da la’akari da nakasar da ke jikinsa ba don ya sami damar biyan bukatun kansa.

An gano saurayin wanda ba a san ko wanene ba a cikin wasu hotuna da aka wallafa a shafin Twitter dauke da kayan hako kasa, yayinda ya daura sandar kugu domin tallafawa ragowar dayan kafar nasa wanda ke da nakasa.

An gano shi yana haƙa magudanar ruwa a ƙarƙashin rana mai zafi a gefen babbar hanya mai cike da jama'a.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel