An damke wani mutum da ya shirya sace matarsa don yin kudi da ita

An damke wani mutum da ya shirya sace matarsa don yin kudi da ita

- Kotu ta tsare wani magidanci Usman Abdulkareem, bisa zarginsa da ake da sace matarsa

- An tattaro cewa Usman ya hada kai da wasu mutane biyu da suka hada da abokinsa da wani boka don yin asiri da matar tasa

- Ya kira matar tasa a waya sannan ya bukaci ta je ta same shi a wani gida wanda yake na bokan ne

Wata kotun Majistare da ke Ilorin a ranar Laraba ta bayar da umarnin tsare Usman Abdulkareem, wanda ake zargi da hada baki da wani mai maganin gargajiya da abokinsa don sace matarsa, a cibiyar gyara hali.

‘Yan sanda sun tuhumi Abdulkareem, wani mai maganin gargajiya, Babatunde Mohammed da wani abokinsa, Fatai Adisa da aikata laifuka biyu na hada baki tare da yin garkuwa da mutum, don aikata kisan kai, wanda hakan ya saba wa sashi na 97 da 274 na dokar kundin shari’a.

Mai shari’a Afusat Alege ta bayar da umarnin a ci gaba da tsare wadanda ake tuhumar a gidan kurkukun Oke-Kura, Ilorin.

An damke wani mutum da ya shirya sace matarsa don yin kudi da ita
An damke wani mutum da ya shirya sace matarsa don yin kudi da ita Hoto: @THISDAYLIVE
Asali: Facebook

KU KARANTA KUMA: Ina nan da raina ban mutu ba – Tsohon kwamishinan yan sandan Kano, CP Muhammad Wakili

Alege ta dage sauraron karar har zuwa ranar 24 ga watan Fabrairu, domin ci gaba da zama, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Dan sanda mai shigar da kara, Sgt. Abubakar Issa, ya fadawa kotu cewa binciken da aka gudanar ya nuna cewa Abdulkareem shine wanda ya kira Mumeenat, matar sa, a wayar tarho sannan kuma ya nemi ta hadu da shi a gidan wanda ake kara na biyu da karfe 5:00 na yamma.

Ya ce binciken da aka gudanar ya nuna cewa Mohammed, boka ne, wanda ke yi wa mutane asirin kudi ta hanyar amfani da sassan jikin dan adam.

Issa ya roki kotu ta dage zaman don baiwa 'yan sanda damar kammala bincikensu.

Sai dai kuma wadanda ake tuhumar, sun musanta aikata laifin.

KU KARANTA KUMA: Hotunan wani gurgu mai kafa daya da ke aikin hako kasa ya ja hankalin jama'a, sun jinjina masa

A wani labarin, tsohon kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Muhammad Wakili wanda aka fi sani da Singam ya yi watsa da rahotannin cewa Allah ya amshi ransa a wani hatsarin mota.

An tattaro cewa wasu labarai sun yadu shafukan zumunta a daren ranar Talata game da zargin mutuwarsa a hatsarin mota, inda mutane suka ta wallafa hotunansa tare da yi masa fatan samun rahamar Allah.

A wata hira da yayi da sashin Hausa na BBC, CP Singam mai ritaya ya bayyana cewa yana nan da ransa kuma cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng