Kungiya ta yi maraba da matakin da Ganduje ya dauka kan Abduljabbar Kabara

Kungiya ta yi maraba da matakin da Ganduje ya dauka kan Abduljabbar Kabara

- Kungiyar MURIC ta yabi Gwamnan Kano na dakatar da Abduljabar Nasiru-Kabara

- Muslim Rights Concern ta ce Gwamnati tayi daidai da aka hana malamin yin karatu

- MURIC ta bukaci a bude makarantar Shehin idan ya amince zai daina barambarama

Kungiyar nan ta Muslim Rights Concern watau MURIC ta yabi gwamnatin Kano a kan dakatar da Sheikh Abduljabar Nasir-Kabara daga yin wa’azi.

MURIC ta fitar da jawabi wanda shugabanta, Ishaq Akintola, ya sa hannu. Jaridar The Cable ta fitar da wannan rahoto a ranar 7 ga watan Fubrairu, 2021.

Farfesa Ishaq Akintola ya ce gwamnatin Abdullahi Ganduje ta yi maganin matsalar da wuri.

Ya ce: “An dade ana kuka da irin karatun da Sheikh Abduljabar Kabara yake yi, kungiyoyin Tijaniyyah da sauran Musulmai ‘yan Ahlul-Sunnah sun koka da shi.”

KU KARANTA: Gwamnatin Kano ta hana Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara wa'azi

“Har ma su na zargin shi da zagin Manzon Allah, Annabi Muhammad (SAW). Wannan abu ne da zai iya jawo Kano da sauran yankin Arewa su barke da rikici.”

“Mun yaba wa gwamna Ganduje da ya yi wa lamarin rigakafi. Hakan zai taimaka Yanzu ba lokaci ba ne da za a bar rikicin addini ya barke.” Inji Farfesa Ishaq Akintola.

Kungiyar ta ce: “Miyagu na nan su na jira rigima ta kaure domin su samu damar yin ta’adi. Za su yi amfani da wannan dama ne su jawo rashin zaman lafiya.”

A dalilin haka ne MURIC ta ke ganin gwamnan Kano ya cancanci yabo. “Mu na fatan sauran gwamnoni za su tashi tsaye, su yi maganin duk wata rigima.”

kKU KARANTA: An zagaye gidan Sheikh Abduljabbar Kabara

Kungiya ta yi maraba da matakin da Ganduje ya dauka kan Abduljabbar Kabara
Sheikh Kabara Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

“Mu na kira ga gwamnatin Kano ta bude masallacin Sheikh Kabara idan ya amince da cewa zai bi doka, zai guje wa yin hudubobi da za su tunzura al’umma.”

MURIC ta bukaci a bada sharuda wajen mukabalar da za ayi, sannan ta ba gwamnati shawara ka da a haska shirin kai-tsaye domin gudun martani daga jama’a.

Shi ma tsohon sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II ya yi magana a kan dambarwar Sheikh Abduljabbar Kabara da gwamnati da malaman jihar Kano.

Malam Muhammadu Sanusi II ya bayyana abubuwan da su ke faru wa a Kano da fitintinu, ya roki Ubangiji ya kawo mafita, tare da kiran mutane su bi koyarwar Sunnah.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel