Sanusi II ya yi kira ga mutanen Kano su tsaya a kan koyarwar Shehu Danfodio

Sanusi II ya yi kira ga mutanen Kano su tsaya a kan koyarwar Shehu Danfodio

- Malam Muhammadu Sanusi II ya yi kira ga al’umma su rike koyawar Sunnah

- Tsohon sarki ya nuna rashin goyon baya ga da’awar Abduljabbar Nasiru Kabara

- Sanusi II ya yabi Malamai da Hukuma a kan dakatar da malamin daga karatu

Tsohon sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II ya yi magana a kan dambarwar Sheikh Abduljabbar Kabara da gwamnati da malaman jihar Kano.

Tsohon sarkin ya yi magana ne wajen karatun littafin Madarijus Salikeen na Ibn Qayyim al-Jawziyyah wanda ya gudanar a ranar Lahadi, 7 ga watan Fubrairu, 2021.

Malam Muhammadu Sanusi II ya bayyana abubuwan da su ke faru wa a Kano da fitintinu, ya roki Ubangiji ya kawo mafita, tare da kiran mutane su tsaya tsayin-daka.

Kamar yadda wani bidiyo da aka wallafa a Twitter ya nuna, an ji Mai martaba ya na cewa Kano kasa ce wanda ta yi riko da koyarwar sunnah ta Shehu Usman Danfodio.

KU KARANTA: Gwamnati ba ta rusa makarantar Sheikh Abduljabbar Kabara ba

“Jama’ar Kano a cigaba da tsayawa a kan cewa ba za mu yarda da komai ba sai abin da Shehu Danfodio ya daura mu a kai, watau tafarkin Ahlul Sunnah wal Jama’a.”

Ya ce: “Dukkanin mutumin da zai zo, ko wanene shi, ya fito mana da wani abu dabam, ya kamata mu nuna masa, Kano ba za ta zama wurin koyar da irin wannan karatu ba.”

A cewar Sanusi II, “Malaman Kano kun kyauta da abin da aka yi.” Sannan ya kara da kiran a guji yin abin da zai kawo tashin hankali; “Kuma a cigaba da zama lafiya.”

“Hukuma kuma a cigaba da ba ta goyon-baya, wannan mataki da gwamnati da gwamna su ka dauka, abin a yaba masu a kai, kuma a goya masu baya ne.” inji shi.

KU KARANTA: Jami'an tsaro sun zagaye gidan Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara

Sanusi II ya yi kira ga mutanen Kano su tsaya a kan koyarwar Shehu Danfodio
Tsohon Sarki Muhammadu Sanusi Hoto: sanusilamidoofficial
Asali: Facebook

A karshe Malam Sanusi II wanda ke zaune a gidansa da ke Landan, kasar Ingila, ya roki Allah ya tsare wa Kano da daukacin al’umma addininsu da akidunsu.

Idan za ku tuna, Sheikh Abdul Jabbar Nasiru Kabara ya yi martani kan dakatarwar da gwamnatin Kano ta yi masa a makon da ya gabata, ya ce an zalunce sa.

Sheihin malamin a wata tattaunawar da aka yi da shi ya ce zaluntarsa gwamnatin ta yi domin ba ta bashi damar kare kansa ba, sai kurum aka hana shi wa'azi.

Babban malamin ya ce tun da yanzu an hana shi karatu a Kano zai dage da yin rubuce-rubuce.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng