Gwamnatin Kano ta hana Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara wa'azi a jihar

Gwamnatin Kano ta hana Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara wa'azi a jihar

- Gwamnatin jihar Kano ta hana wa babban malami Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara yin wa'azi a fadin jihar

- Hakan na zuwa ne sakamakon korafe-korafe da aka shigar na cewa wa'azozinsa na iya haifar da tashin hankali a jihar

- Kazalika, gwamnatin ta kuma hana gidajen rediyo da na talabijin saka karatun malamin har zuwa lokacin da za a kammala bincike a kansa

Majalisar zartaswa na jihar Kano ta dakatar da shahararren malamin addinin musuluncin na jihar Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara daga yin wa'azi a fadin jihar baki daya.

Muhammadu Garba, kwamishinan watsa labarai na jihar Kano ya tabbatarwa BBC matakin inda ya ce an tattauna batun yayin zaman majalisar a ranar Laraba sakamakon wasu rahotanni da ke zargin malamin na furta kalamun da ka iya haifar da tashin hankali a jihar.

Gwamnatin Kano ta hana Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara wa'azi a jihar
Gwamnatin Kano ta hana Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara wa'azi a jihar. Hoto: @TVCnewsng
Source: Twitter

DUBA WANNAN: A kyalle yan Nigeria sun fara mallakar AK 47, Gwamna Ishaku

Ya ce, "gwamnati ta yi nazari kana ta samu rahotanni daban daban har ma daga wasu manyan malamai da hukumomin tsaro, hakan yasa jami'an tsaro kafa kwamiti na musamman don duba kalaman da malamin keyi."

Ya cigaba da cewa bayan tattaunawa kan lamarin da majalisar zartarwa na Kanon ne aka cimma matsayar cewar kalaman malamin na iya tada zaune tsaye don haka aka bayar da umurnin dakatar da shi daga yin wa'azi a jihar.

KU KARANTA: Tofa: Idan yan arewa suka fara rama abinda ake yi wa yan uwansu a kudu abin ba zai yi kyau ba

An kuma bada umurnin rufe masallacin shaihin malamin da ke unguwar Filin Mushe tare da hana shi yin huduba kana an umurci ya guda furta kalaman da ka iya janyo tashin hankali har zuwa lokacin da hukumomin tsaro za su kammala bincikensu.

Har wa yau, gwamnatin jihar Kano ta hana gidajen rediyo da talabijin na jihar saka wa'azinsa ko karatutuka duk dai da nufin tabbatar da zaman lafiya.

Garba ya ce dakatarwa za ta cigaba da aiki har zuwa lokacin da za a kammala bincike sannan a san matakin din din din da za a dauka.

A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.

An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.

Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel