Hukumar DSS ta zagaye gidan Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara

Hukumar DSS ta zagaye gidan Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara

- An ga guggun jami'an tsaro zagaye da gidan malamin darikar Qadiyya a jihar Kano

- Wannan mataki ya biyo bayan umarnin hana malamin gudanar da wa'azi a fadin jihar

- Jami'an tsaron ba su hana kowa shiga ko jajantawa malamin abinda ya faru dashi ba

An ga jami'an tsaro masu yawa a kusa da gidan Sheikh Abdujabbar Nasiru Kabara a Gwale da ke karamar hukumar Gwale a cikin garin Kano.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a safiyar yau Alhamis ne gwamnatin jihar Kano ta sanar da dakatar da shahararren malamin addinin Islama din daga yin wa'azi a jihar saboda salon koyarwarsa da ake ganin yana da matukar tsanani.

Gwamnatin jihar ta kuma bayar da umarnin cewa a rufe dukkan makarantun da malamin ke gudanarwa har sai hukumomin tsaro sun gudanar da bincike.

KU KARANTA: COVID-19: Gwamnatin Kogi ta yi barazanar maka NCDC da PTF a kotu

Hukumar DSS ta zagaye gidan Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara
Hukumar DSS ta zagaye gidan Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara Hoto: The Angle Online
Asali: Facebook

Rahoto ya lura da kimanin motoci biyar na jami'an tsaro masu dauke da manyan makamai, tun daga 'yan sanda zuwa DSS, da jami'an tsaro na NSCDC da sauran wadanda suka kewaye gidan don tabbatar da bin da dokar da aka kafa wa malamin.

Su, duk da haka, basu hana mabiya da masu yi masa jaje shiga gidan ba.

An ga daruruwan mabiya a kewayen gidan da harabar masallacin malamin suna jimami kan matakin Gwamnatin Jihar.

Sheikh Abduljabbar, mabiyin darikar Qadiriyya, ana ganin ya samu sabani tsakanin manyan malamai a jihar.

KU KARANTA: NDLEA ta kame wasu 'yan kasuwa 2 dauke da hodar iblis kilogram 3

A wani labarin, Majalisar zartaswa na jihar Kano ta dakatar da shahararren malamin addinin musuluncin na jihar Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara daga yin wa'azi a fadin jihar baki daya.

Muhammadu Garba, kwamishinan watsa labarai na jihar Kano ya tabbatarwa BBC matakin inda ya ce an tattauna batun yayin zaman majalisar a ranar Laraba sakamakon wasu rahotanni da ke zargin malamin na furta kalamun da ka iya haifar da tashin hankali a jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel