Da duminsa: APC ta yi sasanci tsakanin Yari da Marafa a jihar Zamfara (Hotuna)

Da duminsa: APC ta yi sasanci tsakanin Yari da Marafa a jihar Zamfara (Hotuna)

- Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya yi sasanci tsakanin bangarori biyu na jam'iyyar APC da ke Zamfara

- An yi sasanci tsakanin bangaren tsohon Gwamna Abdul'aziz Yari da kuma bangaren Sanata Kabir Marafa

- Sun sha alwashin hadin kai a jihar domin tabbatar da nasarar jam'iyyar a jihar da kasar nan baki daya

Shugaban kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC, Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya sasanta 'ya'yan jam'iyyar APC na jihar Zamfara.

Sanannen abu ne cewa jam'iyyar APC ta jihar Zamfara ta rabe gida biyu inda aka samu bangaren tsohon gwamnan jihar, Abdul'aziz Yari da kuma bangaren Sanata Kabiru Marafa.

Kamar yadda jam'iyyar APC ta wallafa a shafinta na Twitter, an yi sasanci tsakanin bangarorin biyu na jihar kuma sauran masu ruwa da tsaki sun sha alwashin hada kai a jihar domin ganiin cigaban jihar.

Da duminsa: APC ta yi sasanci tsakanin Yari da Marafa a jihar Zamfara (Hotuna)
Da duminsa: APC ta yi sasanci tsakanin Yari da Marafa a jihar Zamfara (Hotuna). Hoto daga @OfficialAPCNg
Source: Twitter

Da duminsa: APC ta yi sasanci tsakanin Yari da Marafa a jihar Zamfara (Hotuna)
Da duminsa: APC ta yi sasanci tsakanin Yari da Marafa a jihar Zamfara (Hotuna). Hoto daga @OfficialAPCNg
Source: Twitter

KU KARANTA: Hotunan ganawar Zulum ta farko da sabbin hafsoshin tsaro, ya mika manyan bukatu 3

Da duminsa: APC ta yi sasanci tsakanin Yari da Marafa a jihar Zamfara (Hotuna)
Da duminsa: APC ta yi sasanci tsakanin Yari da Marafa a jihar Zamfara (Hotuna). Hoto daga @OfficialAPCNg
Source: Twitter

Da duminsa: APC ta yi sasanci tsakanin Yari da Marafa a jihar Zamfara (Hotuna)
Da duminsa: APC ta yi sasanci tsakanin Yari da Marafa a jihar Zamfara (Hotuna). Hoto daga @OfficialAPCNg
Source: Twitter

KU KARANTA: Barawo ya sace sadaki N100,000 daga aljihun waliyyin amarya a masallacin Al Noor

A wani labari na daban, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ce abun damuwa ne yadda 'yan bindiga ke cin karensu babu babbaka a yankin arewa maso yammacin kasar nan inda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fito daga.

Obasanjo ya bukaci shugaban kasa da ya tashi daga baccinsa kuma ya yaki 'yan bindiga da sauran masu laifuka ballantana a yankin arewacin kasar nan, Punch ta ruwaito.

Tsohon shugaban kasan wanda yayi magana a wata tattaunawar yanar gizo a ranar Lahadi tare da Toyin Falola, ya ce Buhari ya fara tunanin yadda zai bar tarihi mai kyau.

Ya ce, "A tunanina na san Shugaban kasa Buhari saboda yayi aiki tare da ni. Amma na kan tambaya mutane ko dai ban san Buhari bane ko kuma ya sauya daga yadda na san shi ne? Ba wai na yadda da cewa an sauya mana wani Buhari bane daga Sudan da sauran rashin hankali."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel