2023: Dinkewar Yari da Marafa ba barazana bace a gare mu, PDP tayi martani

2023: Dinkewar Yari da Marafa ba barazana bace a gare mu, PDP tayi martani

- Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa ita za ta ci gaba da rike jihar Zamfara a 2023

- A ranar Litinin, 1 ga watan Fabrairu ne aka shirya kungiyoyin adawa da ke cikin APC sannan suka sha alwashin kwato jihar daga hannun PDP

- Sai dai kuma PDP ta bayyana cewa dinkewar kungiyoyin APC din ba zai hana jam’iyyar adawar sake shan kaye ba a 2023

Bayan yin sasanci tsakanin bangarorin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Zamfara, wasu jiga-jigan jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sun jadadda cewa babu abunda zai hana Gwamna Bello Matawalle zarcewa a 2023.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa PDP wacce ke mulki a jihar ta ce hukuncin bangarorin APC na hadewa ba zai shafi nasararta ba a zabe mai zuwa.

Legit.ng ta tattaro cewa gabar da ke tsakanin sansanin tsohon gwamna Abdulaziz Yari da tsohon sanata Kabiru Garba Marafakan zaben fidda gwani na gwamnan APC a jihar a 2019 ne ya ja masu shan kaye.

2023: Dinkewar Yari da Marafa ba barazana bace a gare mu, PDP Zamfara tayi martani
2023: Dinkewar Yari da Marafa ba barazana bace a gare mu, PDP Zamfara tayi martani Hoto: @OfficialPDPNig
Source: Twitter

KU KARANTA KUMA: Korona: Ku yi allurar rigakafi ko ku mutu, FG ta gargadi yan Nigeria

Gwamnan jihar Yobe kuma Shugaban kwamitin rikon kwarya na APC ne ya shirya Yari da Marafa a ranar Litinin, 1 ga watan Fabrairu.

Sai dai kuma wasu masu biyayya ga PDP wadanda suka yi martani kan ci gaban, sun ce sasancin ba zai shafi jam’iyyarsu ba a zaben 2023.

Kakakin PDP a jihar, Alhaji Farouk Ahmad, ya ce:

“Shirinsu ba zai shafi kuri’un da PDP za ta samu ba a zabe mai zuwa. Magoya bayanmu na nan kuma har yanzu muna tare da su. Don haka babu abun tashin hankali.”

Mai ba gwamnan shawara kan harkokin siyasa, Ibrahim Ma’aji Gusau, shima ya ce shirin ba zai shafi nasarar jam’iyyar a jihar ba.

Ya ce:

“Mutane ne za su zabi wanda suke so a karshe. Su za su yanke shawarar zabar A ko B kuma wannan ba zai janye hankalinmu daga abunda muke yi don sauya rayukan jama’a a jihar ba, kuma ma mutane ne ke da ikon yin chanji."

KU KARANTA KUMA: Tsohuwar da bata samu haihuwa ba ta ce ita da kanta ta nema wa mijinta sabuwar mata

A gefe guda, mun ji cewa a watan Maris mai zuwa ne za a sanar da bayyanar wata sabuwar jam’iyya a Najeriya.

Jaridar The Nation ta fitar da rahoto a ranar Laraba, 3 ga watan Fubrairu, 2021 cewa wasu fitattun ‘yan siyasar kasar nan sun hadu, za su kafa jam’iyya.

Daga cikin wadanda ke kan gaba wajen wannan tafiya akwai tsohon shugaban majalisar wakilai, Rt. Hon. Ghali Umar Na’Abba da Olisa Agbakoba SAN.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel