Gazawarka ke addabanka ba kowa ba, PDP ta fadawa Buhari

Gazawarka ke addabanka ba kowa ba, PDP ta fadawa Buhari

- Jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta gargadi gwamnatin Buhari ta daina zargin manyan kasar nan da cin dunduniyarsa

- PDP sun bayyana cewa sakamakon abinda gwamnatinsa ta shuka shi yake girba

- Sun kuma nuna cewa rashin nasara kan lamuran mulkinsa yasa ake sukar gwamnatinsa

Jam'iyyar ta PDP ta ce zargin da Fadar Shugaban kasa ta yi, cewa wasu 'yan Najeriya, musamman fitattu, suna yin kamfen din batanci ga Shugaban kasa, ya nuna cewa mulkin Shugaba Buhari "inuwar rashin nasararsa ke bibiyarsa”, The Nation ta ruwaito.

Fadar Shugaban kasa, ta bakin kakakinta Femi Adesina, ta ce wasu ’yan cin-garin da ba a bayyana sunayensu ba suna ta yin zagon kasa ga Shugaban da manufofinsa.

A wata sanarwa da kakakin ta Kola Ologbondiyan ya fitar a jiya, PDP ta ce: “A bayyane yake cewa gwamnatin APC da Buhari ke jagoranta na fama da gazawa ta kowane bangare a harkokin mulki.

KU KARANTA: Gwamna Ganduje ya ƙaddamar da jami'an kula da dokar Korona 2,000

Inuwar rashin nasararka ita ke bibiyarka, PDP ta fadawa Buhari
Inuwar rashin nasararka ita ke bibiyarka, PDP ta fadawa Buhari Hoto: Herald.ng
Source: UGC

"Idan da gaske yana da wani tarihin nasarori a kowane fanni, Shugaban kasa ba zai roki ‘yan Najeriya ba, ko da a jiharsa ta Katsina da kuma tsakanin mambobin jam’iyyarsa, da su ba shi lambar wucewa."

Majiya ta fidda rahoto cewa fadar shugaban kasa a ranar Juma'a ta gabatar da kararraki kan abin da ta kira shirya makarkashiyar bata sunan Buhari, ta hanyar amfani da wasu jaridu da shafukan yanar gizo.

Mashawarci na Musamman ga Shugaban kasa kan harkokin yada labarai da yada labarai, Femi Adesina, ya yi wannan ikirarin a cikin wata sanarwa mai taken “Kulla makarkashiyar shirya makircin bata sunan Shugaba Buhari.”

Amma PDP ta gargadi fadar shugaban kasa da ta daina raina hankulan 'yan Najeriya kuma ta daina zargin manyan mutane kan gazawar Buhari.

KU KARANTA: Wani magidanci ya dabawa tsohuwar matarshi wuka a gaban kotu

A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayin ganawa da shugabannin hafsoshin kasar a ranar Talata ya ce gwamnatinsa ba ta samu sauki ba wajen cika alkawuran da ta dauka a shekarar 2015, Sahara Reporters ta ruwaito.

A cewar wata sanarwa da Adesina ya fitar, shugaban ya bukaci shugabannin hafsoshin da su kasance masu kishin kasa, yana mai cewa kasar na cikin yanayin neman taimakon gaggawa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel