Ba abu bane mai sauki cika alkawuran da na dauka, in ji Buhari

Ba abu bane mai sauki cika alkawuran da na dauka, in ji Buhari

- Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ba abu ne mai sauki cika dukkan alkawuran da ya dauka wa 'yan Najeriya

- Ya bayyana cewa Najeriya na cikin wani halin neman taimakon gaggawa a fannoni da yawa, musamman tsaro

- Shugaban ya kuma bukaci sabbin hafsoshin soja da su jajirce wajen cimma burin 'yan Najeriya na inganta tsaro

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayin ganawa da shugabannin hafsoshin kasar a ranar Talata ya ce gwamnatinsa ba ta samu sauki ba wajen cika alkawuran da ta dauka a shekarar 2015, Sahara Reporters ta ruwaito.

A cewar wata sanarwa da Adesina ya fitar, shugaban ya bukaci shugabannin hafsoshin da su kasance masu kishin kasa, yana mai cewa kasar na cikin yanayin neman taimakon gaggawa.

Sanarwar ta ambato Shugaban yana fadawa shugabannin hafsoshin, "Muna cikin dokar ta baci. Ku zama masu kishin kasa, ku yi wa kasar aiki da kyau, saboda amincinku ga kasar.

"Kun san matakin da muke a shekarar 2015, kun san matakin da muke yanzu, da kuma ayyukan da muka aiwatar.

KU KARANTA: Gwamnatin tarayya ta fara rabawa mata N20,000 a jihar Kaduna

Yana da matukar wuya mu cika alkawuran da muka dauka, in ji Buhari
Yana da matukar wuya mu cika alkawuran da muka dauka, in ji Buhari Hoto: BBC Hausa
Asali: UGC

"Mun yi alkawarin tabbatar da da tsaro a kasar, farfado da tattalin arziki, da kuma yaki da cin hanci da rashawa. Babu wani abu mai sauki, amma tabbas mun samu ci gaba."

A karshen taron, Irabor, a wata hira da ya yi da manema labarai na fadar gwamnatin, ya ce Buhari ya fada musu cewa abin da ‘yan Najeriya ke fata suna da yawa kuma dole ne su yi duk abin da za su yi don cimma su.

Jaridar Punch ta bada rahoton cewa kungiyar gwamnonin arewa ta tsakiya ta umarci sabbin shugabannin rundunonin da su bullo da sabbin dabaru wadanda zasu magance matsalolin tsaro da suka addabi yankin da kasar baki daya.

KU KARANTA: NIMC ta bai wa MTN, Airtel, da sauran wasu kungiyoyi lasisin yin NIN

Shugaban taron, Abubakar Sani Bello na jihar Neja ya yi wannan kiran a ranar Laraba a cikin wata sanarwa yayin yabawa nadin sabbin shugabannin rundunonin yana mai bayyana hakan a matsayin kyakkyawar shawara da Shugaban kasa ya yanke.

A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba da umarnin sakin dala miliyan 20 nan take, wanda Nijeriya ta yi alkawarin bayarwa a baya ga asusun ajiyar shirin ECOWAS na yaki da ta'addanci a fadin yankin, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban ya sanar da wannan umarni ne a yayin wata gabatarwa ga taron kara wa juna sani karo na 58 na Shugabannin kasashe da gwamnatocin ECOWAS, a Abuja, ranar Asabar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.