Wani magidanci ya dabawa tsohuwar matarshi wuka a gaban kotu
- Wani magidanci ya dabawa tsohuwar matarsa wuka a gaban kotu bayan raba aurensu
- Magidancin ya bayyana kin sa ga raba auren, amma a haka alkali ya raba aurensu
- A halin yanzu magidancin yana hannun 'yan sanda don gudanar da cikakken bincike
‘Yan sanda a ranar Asabar sun cafke wani mutum, Bilyaminu Abdullahi, sakamakon daba wa tsohuwar matar sa, Shafa’atu Sule wuka, jim kadan bayan kotun shariah ta raba aurensu.
‘Yan sanda sun ce lamarin ya faru ne a karamar hukumar Rano da ke jihar Kano.
Kotun ta kuma umarci matar da ta biya Mista Abdullahi N20,000 a matsayin kudin fansar amarya, Premium Times ta ruwaito.
Amma shawarar ba ta yi wa Mista Abdullahi dadi ba don haka ya zaro wuka ya dabawa tsohuwar matar tasa da dan uwanta, Adamu Saleh.
Mista Abdullahi ya roki kotun da kada ta raba auren.
KU KARANTA: Sabbin hafsoshin sojoji sun isa Maiduguri don magance rashin tsaro
Mai magana da yawun ‘yan sanda a Kano, Abdullahi Kiyawa, ya ce tashin hankalin da Mista Abdullahi ya yi ya faru ne a harabar kotun jim kadan bayan hukuncin kotun, yayin da daga baya ya nuna danasanin abinda ya aikata.
Ya bayar da rahoton cewa ba ya son rabuwa da matarsa.
Mista Saleh ya goyi bayan raba auren 'yar uwarsa saboda zargin tashin hankali a cikin gida.
“Yayanta ya zo ya tafi da ita. Na je gidansu amma sun kore ni.
"Na kuma tura amintattu na su shiga tsakani, amma hakan ma bai ba da sakamakon da ake so ba yayin da suka dage kan saki, wanda na ki,” Mista Kiyawa ya ruwaito Mista Abdullahi yana fada a cikin bayanin nasa ga 'yan sanda.
Ms Sule ta bayyana rashin kulawa, cin zarafin jiki da rashin girmama iyayenta a matsayin dalilin neman saki.
Mista Kiyawa ya ce kwamishinan ‘yan sanda, Habu Sani, ya bayar da umarnin a mika karar zuwa sashen binciken manyan laifuka don gudanar da bincike tare da gurfanar da ita a gaban kotu.
KU KARANTA: Wani dan majalisa ya harbe wanda ake zargin dan fashi da makami ne
A wani labarin, Wani dan kasuwa, Abdulkadir Oyeleke, a jiya, ya maka surukinsa, Malam Sani, a gaban Kotun Shari’ar Musulunci da ke zaune a Magajin Gari, Jihar Kaduna, yana neman a karbo masa N69,000, Vanguard News ta ruwaito.
Oyeleke ya fadawa kotun cewa a watan Janairun shekarar 2020, matar Sani, wacce kanwarsa ce, ta ziyarce shi a shagonsa sai ta ga wasu dinkakkun kaya masu kyau kuma ta gaya masa cewa mijinta yana sha'awarsu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng