COVID-19 ta shiga jerin kalubalen duniya kamar ta'addanci, rashawa, in ji Buhari
- Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa akwai bukatar hadin kai don yaki da Korona
- Shugaban ya siffanta Korona da wani kalubale dake addabar duniya kamar sauran ta'addanci
- Shugaban ya bukaci kasashe da su hada kai don samun mafita kan yaduwar Korona
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake jaddada bukatar kasashen duniya su hada kai tare wajen tunkarar cutar COVID-19 kamar sauran kalubalen da ke addabar duniya, Daily Nigerian ta ruwaito.
Da yake jawabi a wajen taron karbar takardun wasikar amincewa da sabbin jakadun Masar, Saudi Arabia da Argentina a fadar shugaban kasa da ke Abuja, a ranar Alhamis, shugaban ya bayyana cewa:
“Muna da kalubale iri daya da ke tasiri sosai ga kasashenmu, wadanda suka hada da ta’addanci, tayar da kayar baya, canjin yanayi, fashewar jama’a, safarar mutane, rashawa, talauci, da kuma yaduwar kananan makamai.
KU KARANTA: Gwamnatin Buhari za ta kashe N204m don kirkirar wata manhaja
“A saman wadannan duka, zango na biyu na annobar COVID-19 ya zo da iri daban-daban da ke haifar da karin kalubale ga bullowar farko.
Shugaba Buhari ya kuma nuna matukar farin cikinsa ga hadin kan da Najeriya da sauran kasashen uku suka samu a wasu fannoni.
“Duk kasashe ukun da aka wakilta a nan suna da kyakkyawar dangantakar bangarori tare da mu.
Jakadun, wadanda suka gabatar da wasikun amincewarsu, su ne: Mista Ihab Moustafa Awad Moustafa daga Jamhuriyar Larabawa ta Masar, Mista Faisal Ebraheem Alajrafi Alghamdi daga Masarautar Saudiyya, da Mista Alejandro Miguel Francisco Herrero daga Jamhuriyar Argentina.
Shugaban ya nanata wa Jakadun shirin na Najeriya "don yin aiki tare da ku baki daya don samun zaman lafiya a duniya, wadatar abinci da muhalli mai dorewa."
Yayin da yake yi wa manzannin fatan alheri a wa'adinsu, ya yi musu fatan su fadada matsayin da suke a yanzu.
KU KARANTA: An sake yiwa Alhaji Atiku Abubakar rigakafin Korona a karo na biyu
"A madadin Gwamnati da jama'ar Najeriya, ina kira gare ku, a yayin gudanar da ayyukanku a Najeriya, da ku dora kan nasarorin magabata da kuma inganta dangantakar 'yan uwantaka tsakanin kasashenmu," in ji shugaban.
Da yake magana a madadin wasu, Amb. Ihab Moustafa ya nuna godiya ga shugaban bisa karbar su da kuma karbar wasikun na su.
Ya tabbatar wa Shugaban kasar da kudurinsu na aiki tare da gwamnatinsa don kara bunkasa da karfafa kawancen kasashen da kawancensu da Tarayyar Najeriya.
"Za mu dogara da irin taimakon da kuke bayarwa da kuma jagora har zuwa wannan," in ji Mista Moustapha.
A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayin ganawa da shugabannin hafsoshin kasar a ranar Talata ya ce gwamnatinsa ba ta samu sauki ba wajen cika alkawuran da ta dauka a shekarar 2015, Sahara Reporters ta ruwaito.
A cewar wata sanarwa da Adesina ya fitar, shugaban ya bukaci shugabannin hafsoshin da su kasance masu kishin kasa, yana mai cewa kasar na cikin yanayin neman taimakon gaggawa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng