Gwamnatin Buhari za ta kashe N204m don kirkirar wata manhaja

Gwamnatin Buhari za ta kashe N204m don kirkirar wata manhaja

- Gwamnatin tarayya ta yadda a ware makudan kudade don kirkirar wata manhajar yanar gizo

- Manhajar za a yi amfani da ita ne wajen kula da hanyoyi da kuma duba ingancinsu

- Ministan ayyuka ya bayyana cewa kirkirar manhajar zai taimaka matuka wajen kula da ingancin hanyoyi a kasar

Gwamnatin tarayya ta amince da a ware makudan kudade da suka kai N204m saboda bude shafin yanar gizo domin sa-ido kan manyan hanyoyin Najeriya, Premium Times ta ruwaito.

Gwamnati ta amince da kashe kudaden domin kwangilar kirkirar wata manhajar da za a rika amfani da ita wajen kula da ayyukan kwangilolin kan hanyoyi da kuma kula da hanyoyin su kan su daga saurin lalacewa da su ke yi.

Ministan Ayyuka na kasa, Babatunde Fashola ya bayyana haka ne a ranar Laraba, bayan gudanar da Taron Majalisar Zartarwa, wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta, cewa za a bada kwangilar ta naira milyan 203,845,333.50.

KU KARANTA: Gani Adams: Kundin tsarin mulki na 1999 shaidanin tsari ne

Gwamnatin Buhari za ta kashe N204m don kirkirar wata manhaja
Gwamnatin Buhari za ta kashe N204m don kirkirar wata manhaja Hoto: Premium Times
Source: UGC

Ya ce manhajar za ta samar da tsari na kula da ayyukan hanyoyi da kuma ingancin ayyukan hanyoyin a Najeriya.

Fashola ya ce manyan hanyoyin gwamnatin tarayya sun yi tsawo da yawan da wata hanyar kamata ya yi a ce ‘yan kwangila kamar biyar ne aka ba aikin yinsa.

Sai yace wannan sabuwar manhajar zata zama kamar wani tabarau na hangen nesan da gwamnatin tarayya za ta rika kulawa da ayyukan da kuma sa ido kan hanyoyi.

“Wannan tsari zai taimaka wajen samar da sauri da gaggawar gyara wuraren da hanyoyin gwamnatin tarayya su ka lalace.

“Zai kuma karfafa masu kulawa da shi har mutum 36 a kowace jiha, tare da daraktocin shiyya su shida.” in ji Fashola.

KU KARANTA: Ba abu bane mai sauki cika alkawuran da na dauka, in ji Buhari

Fashola ya kara jaddawa muhimmancin kirkirar manhajar, inda yake cewa za ta taimaka wajen gane wasu hanyoyin da suka lalace domin a gyara su da wuri.

A wani labarin, Gwamnatin tarayya ta fara raba wa matan karkara kudi Naira dubu 20 a karkashin shirin bayar da tallafi ga matan karkara 4,000 a jihar Kaduna, Daily Trust ta ruwaito.

A cewar gwamnatin tarayya, za a zabi matan 4,000 a fadin kananan hukumomi 23 na jihar.

An gabatar da shirin a cikin shekarar 2020 don ci gaba da aiwatar da tsarin zamantakewa a Gwamnatin Shugaba Buhari.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel