An sake yiwa Alhaji Atiku Abubakar rigakafin Korona a karo na biyu
- Mai taimakawa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya bayyana cewa an sake yiwa Atiku rigakafin Korona
- A baya can an yiwa tsohon mataimakin shugaban kasan rigakafin a ranar 6 ga watan Janairu
- Allurar da aka yi masa ta shahara a duniya, Najeriya tuni tana shirin jigilarta a watan Fabrairu
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ya sake yin rigakafin Korona Pfizer-BioNTech COVID-19 Kashi na biyu, jaridar The Nation ta rahoto.
Mai taimaka masa a fannin yada labarai Paul Ibe ya tabbatar da hakan.
Tsohon mataimakin shigaban kasa da a halin yanzu yana Dubai, Hadaddiyar Daular Larabawa, ya yi allurar ta farko a ranar 6 ga Janairu.
KU KARANTA: Ba abu bane mai sauki cika alkawuran da na dauka, in ji Buhari
“H.E @atiku da sanyin safiyar yau yayi rigakafin Covid-19 na Pfizer-BioNTech na biyu. A baya ya yi rigakafin farko a ranar 6 ga watan Janairu,” Ibe ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Alurar ta Pfizer-BioNTech COVID-19 ta samu karɓuwa daga ƙasashe da dama, ciki har da Amurka da Ingila.
Najeriya za ta fara jigilar allurar rigakafin a watan Fabrairu, a cewar shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya Kayode Fayemi.
KU KARANTA: Gani Adams: Kundin tsarin mulki na 1999 shaidanin tsari ne
A wani labarin, Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya karbi allurar rigakafin cutar COVID-19.
Ana ganin cewa shine dan Najeriya na farko da ya karbi rigakafin.
The Cable ta ruwaito mai magana da yawun Atiku, Paul Ibe, ya bayyana hakan ranar Alhamis. Atiku ya yi nasa alluran ne a Dubai, hadaddiyar daular larabawa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng