Gwamnatin tarayya ta fara rabawa mata N20,000 a jihar Kaduna

Gwamnatin tarayya ta fara rabawa mata N20,000 a jihar Kaduna

- Gwamnatin tarayya ta fara raba wa matan jihar Kaduna kudin tallafi N20,000

- An bayyana cewa, za a tallafawa matan ne a fadin kananan hukumomi 23 a jihar Kaduna

- Gwamnatin jihar Kaduna ta yabawa gwamnatin tarayya na yunkurin tallafawa mata

Gwamnatin tarayya ta fara raba wa matan karkara kudi Naira dubu 20 a karkashin shirin bayar da tallafi ga matan karkara 4,000 a jihar Kaduna, Daily Trust ta ruwaito.

A cewar gwamnatin tarayya, za a zabi matan 4,000 a fadin kananan hukumomi 23 na jihar.

An gabatar da shirin a cikin shekarar 2020 don ci gaba da aiwatar da tsarin zamantakewa a Gwamnatin Shugaba Buhari.

Babban Sakatare, Bashir Nura Alkali, ya wakilci Ministar jin kai da Harkokin Ci Gaban Jama'a a taron bude shirin da aka gudanar a Jihar Kaduna.

KU KARANTA: Inganta asibitoci ya fi sayen rigakafin COVID-19, Bill Gates ga Buhari

Gwamnatin tarayya ta fara rabawa mata N20,000 a jihar Kaduna
Gwamnatin tarayya ta fara rabawa mata N20,000 a jihar Kaduna Hoto: National Accord Newspaper
Asali: UGC

Ya bayyana cewa “ya yi daidai da hangen nesa game da kasa na Shugaba Muhammad Buhari na fitar da 'yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci cikin shekaru 10.

Ya ce an tsara shirin ne don samar da tallafi sau daya ga wasu mata masu karamin karfi da masu rauni a yankunan karkara da birane na kasar.

“Za a raba tallafin kudi na N20,000.00 ga mata masu karamin karfi kimanin 125,000 a fadin Jihohi 36 na Tarayya da Babban Birnin Tarayya.

“Burinmu a Jihar Kaduna shi ne bayar da tallafin ga sama da mutane 4,000 a fadin kananan hukumomin 23.” inji shi.

A nata jawabin, mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna, Hadiza Balarabe ta ce “COVID-19 har yanzu yana yin mummunan tasiri a rayuwar mutane musamman mata.

Ta ce bayar da kudin babu shakka zai kawo taimako ga mata a cikin al'umma, musamman wajen karfafa kudaden shigansu.

KU KARANTA: Sojojin Najeriya sun mamaye sansanonin Boko Haram dake dajin Sambisa

A wani labarin, Kungiyar Kare Hakkin Tattalin Arziƙi da Ayyukan Amana (SERAP) ta bukaci Ministan Harkokin Jin Kai da Ci Gaban Jama’a, Hajia Sadiya Umar Farouq, ta “buga bayanan yadda ake shirin biyan Naira biliyan 739 zuwa ga miliyan 24.3 na talakawa na tsawon watanni shida”.

Kungiyar ta nemi a ba da cikakkun bayanan ne a kan takardar ‘Yancin Ba da Bayani (FoI), a ranar 23 ga Janairun 2021, dauke da sa hannun Mataimakin Darakta Kolawole Oluwadare.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel