Inganta asibitoci ya fi sayen rigakafin COVID-19, Bill Gates ga Buhari

Inganta asibitoci ya fi sayen rigakafin COVID-19, Bill Gates ga Buhari

- Wani babban ba'amurke mai taimakon jama'a ya bai wa Najeriya shawara kan sayen rigakafin Covid-19

- Ya bayyana cewa Najeriya ba ta bukatar sayen allurar a wannan lokaci da take fama da karancin kudade

- Ya kuma shawarci kasar da ta zuba kudaden wajen farfado da asibitoci na matakin farko a kasar

Wani Ba’amurke mai taimakon jama’a kuma wanda ya kirkiro Microsoft, Bill Gates, ya ce Najeriya ba ta bukatar kashe makudan kudi wajen sayen alluran rigakafin COVID-19.

Ya bayyana cewa kamata ya yi ta fi mayar da hankali kan farfado da bangaren kiwon lafiya musamman tagayyararrun cibiyoyin kula da lafiya na matakin farko.

Gates ya fadi haka ne yayin da yake amsa tambayar da jaridar The PUNCH ta yi a yayin wata hira da zababbun ‘yan jaridar Afirka a ranar Talata.

KU KARANTA: Makiyaya sun tattara nasu-ya-nasu daga jihar Ondo sun cilla Ekiti

Gyara asibitoci ya fi sayen rigakafin COVID-19 - Bill Gates ga FG
Gyara asibitoci ya fi sayen rigakafin COVID-19 - Bill Gates ga FG Hoto: Vanguard News
Asali: UGC

Ministan Lafiya, Dokta Osagie Ehanire, a cikin watan Disamba ya sanar da majalisar dattijai cewa Najeriya za ta bukaci sama da N400bn don yin rigakafin kashi 70 na yawan mutanen Najeriya a kan dala 8 a kowace allura.

Lokacin da aka tambaye shi ko ya dace Najeriya ta kashe irin wannan makudan kudade wajen sayen allurar rigakafi a tsakanin sauran matsalolin da suka addabi fannin kiwon lafiya, Gates ya ce,

“Babu shakka tasirin saka kudi cikin harkar lafiya musamman tsarin kula da lafiya na farko zaiyi matukar girma ta fuskar kiyaye rayukan yara kuma kunada gaskiya.
"Bai kamata Najeriya ta karkatar da karancin kudin da take da shi ba ga lafiya ga kokarin biyan kudin allurar rigakafin ta COVID mai matukar tsada."

Gates ya ce Najeriya za ta iya dogaro sosai da kungiyoyi irin su GAVI da allurar kawancen rigakafin COVID-19.

Ya yi jayayya cewa saka hannun jari a cikin tsarin kiwon lafiya na matakin farko zai inganta ɗaukar mataki da gina Nijeriya wajen magance sauran cututtuka.

Lokacin da aka tambaye shi ko gidauniyarsa za ta taimaka wa Najeriya wajen samar da alluran rigakafin COVID-19, Gates ya ce irin wannan matakin za a kunsa shi cikin shirin shekaru biyar.

KU KARANTA: Wani dan kasuwa ya maka surukinsa a kotu a kan N69,000

A wani labarin daban, Wata tawagar masu bincike a Jami'ar Ilorin (UNILORIN) sun gano karfin Bromelain wanda aka samo daga 'ya'yan itacen abarba don rage karfin kwayar cutar COVID-19, Vanguard ta ruwaito.

A cewar Jami'ar Ilorin a wata sanarwa da aka bayar a ranar Litinin, binciken ya kasance tare da Farfesa Bamidele Owoeye, Shugaban, Sashin Ilimin Kimiyyar Jiki, da Mista Ahmed Bakare, dalibin PhD a jami'ar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.