Sojojin Najeriya sun mamaye sansanonin Boko Haram dake dajin Sambisa

Sojojin Najeriya sun mamaye sansanonin Boko Haram dake dajin Sambisa

- Sojojin Najeriya sun afkawa sansanin 'yan ta'addan Boko Haram a dajin Sambisa

- Harin ya biyo bayan sa'o'i kadan da aka nada sabbin hafsoshin sojojin Najeriya

- Sojojin sun bayyana cewa sun wargaza sansanin 'yan ta'adda 4 a yankin na Sambisa

Sojojin Najeriya tare da goyon bayan kungiyar hadin gwiwa ta Multinational Joint Taskforce, MNJTF, sun mamaye wasu yankuna hudu na Boko Haram a Arewa maso Gabas.

An bayyana nasarar ne 'yan sa'o'i bayan sanarwar sabbin hafsoshin soja.

Aikin da Brig. Gen Waidi Shaibu, Birgediya kwamandan runduna ta musamman ta 21, ya afkawa mayakan Boko Haram da dama a Maiyanki, Darulsallam, Bula Kurege da Izza.

Wata majiyar soji ta fadawa PRNigeria cewa sansanonin sun kasance sansanin horar da mayakan kungiyar tare da girke dakaru masu shirin ko-ta-kwana a shirye-shiryen kai harin kwanton bauna a wuraren sojojin da ke kusa.

KU KARANTA: Wata bakuwar cuta ta fara kashe mutane a jihar Sokoto

Sojojin Najeriya sun mamaye sansanonin Boko Haram dake dajin Sambisa
Sojojin Najeriya sun mamaye sansanonin Boko Haram dake dajin Sambisa Hoto: TRT World
Asali: UGC

Majiyar ta ce an kashe wasu kwamandojin kungiyar 'yan ta'addan da kuma mayaka masu yawan gaske, yayin da yawa kuma suka samu munanan raunuka yayin kai harin.

An kame dimbin kayan aiki daga hannun ‘yan ta’addan yayin da kayan abinci, Na’urar abubuwan fashewa, Bama-bamai, abubuwan dinkin kayan sawa duk an lalata su.

“Mun share Maiyanki, Darulsallam, Bula kurege kuma yanzu mun karbe Izza, dukkansu tsoffin wuraren Boko Haram ne masu karfi. Sojojinmu sun sha kai hari mafakarsu, cikin dare, amma duk an fatattake su yayin da aka yiwa makiyan mummunar rauni.

Ya kuma bayyana cewa soja daya ne ya rasa rayuwarsa yayin da sojoji uku suka ji rauni.

KU KARANTA: Inganta asibitoci ya fi sayen rigakafin COVID-19, Bill Gates ga Buhari

A wani labarin, Makarantar Tsaro ta Najeriya (NDA) ta ba da sanarwar buɗe kofarta don shiga cikin kwas na 73 na yau da kullum.

Masu sha'awar neman shiga makarantar na iya nema daga 23 ga Janairu zuwa 24 Afrilu, a cewar Magatakardar Makarantar, Brig.-Gen Ayoola Aboaba.

Aboaba, a cikin wata sanarwa a daren Lahadi, a Kaduna, ya ce an bude karbar shiga ne ga duk wadanda suka cancanta maza da mata ‘yan Najeriya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.