Babu cutarwar da za ta sami Bishop Kukah - CAN

Babu cutarwar da za ta sami Bishop Kukah - CAN

- Kungiyar CAN ta gargadi Musulmai da su kau da idanunsu a kan Bishop Mathew Kukak

- Sun kuma yi kira ga jami'an tsaro da su tabbatar da babu wani abu da zai same shi

- CAN ta bayyana amincewa da goyon bayan Kukah kan jawabansa na Kirsimeti

Kungiyar Kiristocin Najeriya ta gargadi wadanda ke yi wa Bishop din Katolika na Sakkwato, Dakta Matthew Kukah, gargadi, da su daina ayyukansu na “haramtacciyar hanya” sannan ta nemi hukumomin tsaro da su tabbatar da tsaron malamin.

Kungiyar ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da Sakataren ta, Joseph Daramola, ya bayyana wa manema labarai a ranar Alhamis.

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa wata kungiya da ke Sakkwato ta nemi Kukah da ya bar jihar ko kuma gabatar da hakuri game da kalaman da ya yi game da addinin Islama.

KU KARANTA: Hadarin hanyar Bauchi ya yi sanadiyyar rayukan mutane 21 daga cikin fasinjoji 22 - FRSC

Babu cutarwar da za ta sami Bishop Kukah - CAN
Babu cutarwar da za ta sami Bishop Kukah - CAN Hoto: The Guardian
Asali: UGC

Wani bangare na sanarwar ya bayyana cewa CAN na sane da duk abubuwan da ke faruwa. Sun bayyana masaniyarsu da bayanan da Kukah ya yi a lokacin bikin Kirsimeti

Kungiyar CAN ta kuma ta san "yadda wasu gungun mutane suka yi ta yi masa barazana da duwatsu yayin da duk hukumomin tsaro da abin ya shafa suna yin kamar babu wani abu mai ban mamaki da ke faruwa.

“Muna mamakin shin wadanda ke yi wa Bishop din Katolika na Sakkwato barazana sun fi karfin doka ko kuma su wasu ne masu tsarki a kasar.

“Mun yi nazarin duk sakon Kirsimeti na Dr Kukah kuma har yanzu ba mu ga wani abin da zai tayar da hankali ga Musulunci ko wadanda ba Kiristoci ba.

"Ba mu ga wani abu mara kyau ba a cikin sakon da ya aike wa al’ummar kasar nan wadanda suka jarabtu da ‘yan ta’adda, makiyaya, 'yan fashi da masu satar mutane kamar babu gwamnati a ciki.

"Ba mu ga wani abu da ba daidai ba a gaya wa gwamnatin wanda nade-naden mukaminta ya saba wa Kiristoci da duk gaskiya.

“Idan sukar da ake yi wa Shugaban Musulmai a yau, ta haifar da tashin hankali ne ga Musulunci, to hakan na nufin wadanda ke sukar lamirin tsoffin Shugabani Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan lokacin da suke kan mulki hakika suna fada ne da Kiristanci.

“Yaushe ya zama laifi in faɗi gaskiya ga gwamnati? Yaushe ya zama laifi ga sukar wata gwamnati a kasar?

CAN ta yi mamakin dalilin da ya sa jami'an tsaro suka kasa cafke wadanda ke barazanar kai wa Bishop din hari,.

CAN tace, “Yaushe 'yan sanda da Daraktan Hukumar Tsaron Kasa suka rasa ikonsu ga bata gari da marasa bin doka da ke ta yin alfahari da rashin bin doka ba tare da kalubale ba?

"Muna mamakin shin waɗancan ƙungiyoyin musulmin da suke barazanar maganin Kukah da sun sami amsa daidai daga takwarorinsu na Krista, shin ba za mu qona ƙasar ba ne?

“Papacy ce ta tura Bishop Kukah aiki a Sakkwato kuma yi masa barazana yin barazana ce wa duniyar Kiristanci.

"A wannan kasar, muna da malami na Katolika wanda sunansa ya yi daidai da Shugaba Muhammadu Buhari amma Cocin Katolika ba ta ga ya kamata ta sanya masa takunkumi ba saboda 'Yancin Magana da Hadin Kai ba batun tsarin mulki ba ne kawai na al'amarin Allah ne."

“Muna kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da dukkan jami’an tsaro da su tabbatar da cewa babu wata cuta da za ta sami Bishop din Katolika na Diocese na Sakkwato, Dakta Matthew Hassan Kukah.

"Dangane da batun kungiyar Kiristocin Najeriya, abin da ya fada a lokacinKirsimeti yana cikin yanayi na doka.

KU KARANTA: WHO ta dira Wuhan don bincike kan Korona

“Lokaci ya yi da wadanda za su buya a karkashin ra’ayin addini don inganta rikici da rikice-rikice su daina yin hakan idan muna son kasar nan ta ci gaba.

"Mun gaji da zub da jini a kasar nan kuma muna kira ga jami'an tsaro da su tashi tsaye wajen sauke nauyin da tsarin mulki ya dora musu. Babu wani abin da zai faru da Bishop Matthew Hassan Kukah. Ya isa haka."

A wani labarin, Revd. Matthew Kukah, bishop na Katolika na Sakkwato, ya sake caccakar gwamnatin Najeriya.

Kukah a cikin hudubarsa ta baya-bayan nan ya koka kan yadda Najeriya ta zama kazamar kasa, cike da tarkace, yaudara, karya, cin amana, da kuma rikita-rikita inda duhu ya mamaye komai.

Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 6 ga watan Janairu, yayin da yake gabatar da hudubarsa a babban cocin Katolika na St Joseph, Kaduna, a lokacin da ake gudanar da hidimar Archbishop Peter Yariyock Jatau, Archbishop na Kaduna Catholic Diocese.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel