El-Rufai ya saki N100m don yaran da ke fama da tamowa a Kaduna

El-Rufai ya saki N100m don yaran da ke fama da tamowa a Kaduna

- Gwamnatin jihar Kaduna ta saki N100m domin yaki da tamowa a fadin jihar

- Gwamnatin ta kara bayyana cewa tana shirye-shiryen bunkasa tallafin

- Gwamnatin ta bayyana sake kudin a kananan hukumomi 15 da unguwanni 77 a fadin jihar

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya amince da fitar da Naira miliyan 100 don sayo Sarrafaffen Abinci mai Gina Jiki (RUTF) da ake bukata don kula da yara masu fama da tamowa.

Salisu Lawal, Daraktan, Hukumar Kula da Taimakon Bunkasa, Tsare-tsare da Kasafin Kudi, ya bayyana haka a wata hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Kaduna ranar Alhamis.

Ya bayyana cewa ma'aikatar kudi ta jihar ta saki adadin da aka amince da shi a ranar 31 ga Disamba, 2020.

Ya kara da cewa “nan ba da dadewa ba, za mu sayo Sarrafaffen Abinci mai Gina Jiki (RUTF) da kuma samar da wasu rukunin Samarwa Al'umma abinci mai maganin Matsanancin Tamowa (CMAM) don tserar da yaranmu daga mutuwa da kuma rashin abinci mai gina jiki."

KU KARANTA: Pantami: Shin za a rufe layin wadanda basu hada SIM dinsu da NIN ba?

El-Rufai ya saki N100m don yaran da ke fama da tamowa a Kaduna
El-Rufai ya saki N100m don yaran da ke fama da tamowa a Kaduna Hoto: UGC/African Studies Center
Asali: Facebook

“Gwamnati tana aiki don tattara dukiyar da ake bukata don magance matsalar rashin abinci mai gina jiki a jihar.

"Tana aiki musamman don inganta hanyoyin magidanta na rayuwa ta hanyar aiwatar da shirye-shiryen kare zamantakewar jama'a da nufin karfafawa iyalai damar wadatar da yaransu yadda ya kamata."

Jami'in kula da abinci mai gina jiki na jihar, Ramatu Haruna, ta ce gwamnati ta iya magance 15,329 daga cikin yara 21,265 da ke fama da tamowa daga watan Janairu zuwa Satumba na 2020.

Misis Haruna ta ce ana aiwatar da shirin na CMAM a kananan hukumomi 15, wanda ya hada da unguwanni 77.

Ta kara da cewa an kafa cibiyoyin kwantar da hankali a manyan asibitocin 17, ciki har da 44 Army Reference Hospital, Kaduna, don kula da Tsananin Tamowa mai fama da matsalar rashin lafiya.

Isah Ibrahim, mai ba da shawara kan harkokin abinci mai gina jiki, na kungiyar agaji ta Save the Children International, ya yaba wa gwamnatin jihar kan tsabar kudaden da ta ke tallafa wa dashi, yana mai bayyana ta da cewa "ta yi daidai da lokaci" don hana aukuwar mace-mace.

KU KARANTA: Tsarin zaben Amurka yafi na kasashen duniya ta uku muni -Trump

“Wannan wani bangare ne na shawarwarinmu, kuma kungiyar Save the Children tana matukar farin ciki da martanin da gwamnatin da El-Rufa’i ke jagoranta wajen ceton rayukan yara 'yan kasa da shekaru biyar daga mutuwar da za a iya kiyayewa.

"Muna sa ran karin fitarwa da kuma samun tallafin kudi na abinci mai gina jiki don tabbatar da cikakken aiwatar da ayyuka a jihar."

A wani labarin kuwa, Domin murnar shiga sabuwar shekara, gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi umurnin sakin fursunoni 12 daga cibiyoyin gyara hali a jihar, jaridar The Cable ta ruwaito.

A wata sanarwa daga Muyiwa Adekeye, mai ba E-Rufai shawara na musamman a kafofin watsa labarai da sadarwa, ya nuna cewa an yi wa wadanda suka ci moriyar shirin bisa ga shawarar kwamitin bayar da shawarwari kan afuwa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.