Yanzu yanzu: NECO ta fitar da sakamakon jarrabawar SSCE

Yanzu yanzu: NECO ta fitar da sakamakon jarrabawar SSCE

- Hukumar shirya jarrabawar kammala babban sakandare ta Najeriya, NECO, ta saki sakamakon jarrabawar bana

- Shugaban hukumar, Farfesa Godswill Obioma ne ya bada sanarwar hakan a hedkwatar hukumar da ke Minna

- Ya kuma sanar da cewa hukumar ta soke wasu cibiyoyin rubuta jarrabawar 12 a wasu jihohi saboda samunsu da aikata magudin jarrabawa

Hukumar Jarrabawa ta Kasa wato (NECO) ta fitar da sakamakon Jarrabawar Dalibai da suka kamalla babban sakandare wato SSCE, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Sakamakon ya nuna cewa adadin daliban da suka samu nasarar samun credit a darrusa biyar ko fiye da hakan ya karu da kashi biyu cikin 100.

Yanzu yanzu: NECO ta fitar da sakamakon jarrabawar SSCE
Yanzu yanzu: NECO ta fitar da sakamakon jarrabawar SSCE. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Dukkanku dajin Sambisa za ku garzaya, Buratai ga sojin da ake horarwa

Shugaban hukumar, Farfesa Godswill Obioma ne ya sanar da hakan a Hedkwatar ta Hukumar NECO da ke Minna a Jihar Niger.

Hukumar ta kuma soke wasu cibiyoyin rubuta jarrabawa 12 saboda samunsu da hannu wurin tafka magudin jarrabawa.

KU KARANTA: Sojoji 6 sun rasu sakamakon artabu da suka yi da 'yan bindiga a Katsina

Ya ce makarantun da aka hana rubuta jarrabawar sun hada da hudu a Jihar Adamawa, biyu a Kaduna, biyu a Katsina, daya a Taraba sannan daya a babban birnin tarayya, Abuja.

A wani labarin daban, kun ji kungiyar samari masu kishin aljihunsu da ake kira Stingy Men Association (SMAN) a turance tana samun bunkasa inda ake ta bude rassa a kasashen duniya daban-daban, BBC Hausa ta ruwaito.

A ranar Litinin 11 ga watan Janairun shekarar 2020 ne kungiyar ta bude shafinta na musamman a kafar Twitter da Facebook tare da tamburi a Najeriya.

Wasu kasashen Afirka sun bi sahun Najeriya sun bude rassan kungiyar a kasashensu, kasashen sun hada da Ghana, Liberia, Uganda, Malawi da Zambia.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel