Sojoji 6 sun rasu sakamakon artabu da suka yi da 'yan bindiga a Katsina

Sojoji 6 sun rasu sakamakon artabu da suka yi da 'yan bindiga a Katsina

- Dakarun sojojin Najeriya shida sun rasu yayin gumurzu da 'yan bindiga a jihar Katsina

- Sojojin sun yi yunkurin datse yan bindigan ne da ke kokarin shiga daji hakan yasa suka yi musayar wuta

- Sojojin basu lura ba ashe akwai wasu yan bindigan da suka buya a kan bishiyoyi kuma suke bude musu wuta

A kalla dakarun sojoji shida ne suka riga mu gidan gaskiya yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon gumurzun da suka yi da yan bindiga a kusa da Faskari Marabar Maigora da ke Jihar Katsina.

Yan bindigan sun kuma sace bindigu da harsashin sojojin da suka kashe.

Majiyoyi kwarara sun shaidawa majiyar Legit.ng cewa lamarin ya faru ne misalin karfe 8.20 na safen ranar Lahadi yayin da dakarun sojojin suka yi yunkurin datse yan bindigan da ke hanyarsu na shiga daji.

'Yan bindiga sun kashe sojoji shida a Katsina
'Yan bindiga sun kashe sojoji shida a Katsina. Hoto: MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Sarkin Billiri, Dr Abdu Buba Maisheru II (Mai Tangale) ya mutu

"Sojojin ba su san cewa 'yan bindigan sun girke wasu daga cikin mambobinsu a kan bishiyoyi kuma suka bude musu wuta. Daga bisani yan bindigan sun samu kwarin gwiwa suka bude wa sojojin wuta," a cewar wani majiya wanda ke da bayani kan faruwar lamarin.

Majiyar ya ce dakarun sojojin saman Najeriya, NAF, ne suka kawo wa sojojin dauki da jiragen su na sama inda suka tarwatsa yan bindigan.

KU KARANTA: Dukkanku dajin Sambisa za ku garzaya, Buratai ga sojin da ake horarwa

Rundunar sojin Najeriya, a ranar Lahadi ta sanar da cewa dakarunta na Operation Hadarin Daji sun kashe a kalla yan bindiga 50 a kauyen Kuriya da ke karamar hukumar Kaura Namoda a jihar Zamfara, a cewar Hedkwatar Tsaro.

Hedkwatar ta Tsaro ta kuma ce sojojin sun kwato shanu 334 da yan bindigan suka sace daga hannun al'umma yayin gumurzun.

A wani labarin daban, rikici ya kaure a zauren majalisar Jihar kasar Ghana a jiya Laraba 6 ga watan Janairu bayan rushe majalisar kunshi ta bakwai.

A cikin hoton bidiyon da ya karade shafukan dandalin sada zumunta, an gano rikici ne ya kaure tsakanin yan jam'iyyar NPP da NDC kan wacce jam'iyya ne ke da rinjaye kuma wacce zata fitar da sabon Kakakin Majalisa.

Kamar yadda bidiyon ya nuna, wasu daga cikin yan majalisar sun rika kai wa juna hannu sannan wasu suka rika fatali da akwatunan kada kuri'a da ke zauren majalisar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164