Bayan Nigeria, an bude kungiyar samari masu 'dunƙule hannu' a kasashe 5
- Kungiyar samari masu matse aljihu ta fara bunkasa zuwa sauran kasashen Afirka
- Wasu daga cikin kasashen da suka bude rassan kungiyar sun hada da Ghana, Liberia, Uganda, Malawi da Zambia
- A ranar Litinin ne kungiyar ta bude shafinta na musamman a dandalin sada zumunta na Twitter
Kungiyar maza masu rowa da ake kira Stingy Men Association (SMAN) a turance tana samun bunkasa inda ake ta bude rassa a kasashen duniya daban-daban, BBC Hausa ta ruwaito.
A ranar Litinin 11 ga watan Janairu ne kungiyar ta bude shafinta na musamman a kafar Twitter da Facebook tare da tamburi a Najeriya.
DUBA WANNAN: Mai garkuwa ya biya N1.5m don fansar kansa daga hannun 'yan bindiga da suka sace shi
Wasu kasashen Afirka sun bi sahun Najeriya sun bude rassan kungiyar a kasashensu, kasashen sun hada da Ghana, Liberia, Uganda, Malawi da Zambia.
Samari da dama sunyi ta fitowa suna nuna goyon bayansu ga kungiyar da manufofinta inda wasu suka rika wallafa katin shiga kungiyar da matsayinsu a shafukansu.
Wasu daga cikin manyan mawakan Najeriya suma ba a bar su a baya ba wurin shiga kungiyar cikinsu akwai mai kamfanin waka ta Mavin Records, Don Jazzy.
Shima mawaki Mr Eazi dan asalin Najeriya amma mazaunin Landan ya wallafa kattinsa na shaidar zama da kungiyar samarin masu rowa a shafinsa na Twitter.
DUBA WANNAN: Dukkanku dajin Sambisa za ku garzaya, Buratai ga sojin da ake horarwa
Mutane da dama sun yi ta yi wa juna barkwanci tare da yin nishadi game da kafuwar kungiyar da yadda zata sauya alakar 'yan mata da samarinsu.
KU KARANTA: Mai garkuwa ya biya N1.5m don fansar kansa daga hannun 'yan bindiga da suka sace shi
Kawo yanzu ba a san takamammen wadanda suka kafa kungiyar ba, duk da cewa cikin raha an fara zancen kafa babban ofishin kungiyar a nan gab
A wani labarin daban, wani mai siyar da magani, Chidinma Ikechukwu Omah, wanda budurwarsa ta cinnawa wuta a rukunin shagunan Wadata a Makurdin Jihar Benue ya rasu, The Nation ruwaito.
Omah wanda aka ruwaito ya rasu da misalin karfe 10:00 na daren Litinin sanadiyar mummunar konewar da yayi bayan budurwarsa, Esther Alex, ta zazzaga masa fetur tare da cinna masa ashana da misalin karfe 2:00 na ranar Litinin din.
Mai magana da yawun hukumar yan sandan Benue, DSP Catherine Anene, ta tabbatar da faruwar lamarin ga wakilin mu a Makurdi.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng