Daliban da ke goyon bayan Bola Tinubu a 2023 sun zabi Shugabannin kungiya

Daliban da ke goyon bayan Bola Tinubu a 2023 sun zabi Shugabannin kungiya

- Kungiyar ANSSO ta ce tana tare da Bola Tinubu a zabe mai zuwa na 2023

- ANSSO ta kafa shugabanni da za su yi kokarin ganin Tinubu ya kai labari

- Giwa Murtala ne zai jagoranci NEC yayin da John Abba yake rike da NAC

Majalisar NAC ta kasa ta kungiyar National Students Support Organisation, ANSSO, ta zabi shugabannin da su jagoranci al'amuranta.

Wannan kungiyar ta magoya bayan Asiwaju Bola Ahmed Tinubu tana kokarin ganin jagoran na jam’iyyar APC ya zama shugaban kasa a 2023.

Jaridar Vanguard ta rahoto shugaban majalisar mashawarta ta wannan kungiya, John Abbah, ya na cewa an kafa ANSSO ne domin yi wa Bola Tinubu yaki.

Mista John Abbah ya ce dalibai daga fadin jihohin Najeriya masu kishin kasa da son cigaba da jagoranci nagari ne su ka kafa kungiyar ANSSO.

KU KARANTA: Akwai magana a kasa tsakanin Buhari da Tinubu tun tuni

Abbah ya ke cewa kungiyarsu ta fahimci babu wanda ya fi dacewa ya rike Najeriya a wannan zamani irin jigon APC, Asiwaju Bola Tinubu.

Kungiyar za ta tsaya sai inda karfinta ya kare wajen ganin tsohon gwamnan na Legas ya yi takarar kujerar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC a zabe mai zuwa.

‘Ya ‘yan wannan kungiya sun hada da: Sakatarenta, Adeyemi Azeez Amoo, Hon. Akanbi Afonja, Malam Ibrahim Ibrahim, Hon. Tayo Sanyaolu, da Hon.Esinrogunjo Musbau.

Ragowar sune: Kwamred Bala Mohammed Oshoke, Hon. Adebogun Adedayo, Hon. Onyedika Agbo, da kuma Kwamred Mukhtar Akosh.

KU KARANTA: Abin da zai faru da takarar Tinubu - Fasto

Daliban da ke goyon bayan Bola Tinubu a 2023 sun zabi Shugabannin kungiya
Bola Tinubu Hoto: www.premiumtimesng.com
Source: UGC

An zabi shugabannin jihohi da shiyyoyi, an yarda Kwamred Giwa Murtala ne zai jagoranci majalisar koli ta kungiyar magoya bayan na Asiwaju Bola Tinubu.

A karshen makon da ya wuce kuma kun ji cewa gadar Shugaban kasa tayi magana game da kiran da ake yi na cewa ya kamata a sauke shugabannin sojojin Najeriya.

Garba Shehu ya bayyana abin da ya sa aka bar hafsun sojojin na tsawon shekaru biyar, amma kalaman Hadimin Shugaban kasa sun jawo an yi masa kaca-kaca.

Dattawan Najeriya sun yi wa Garba Shehu raga-raga bayan ya fito ya kare mai gidansa, Buhari.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel