Abin da ya hana Shugaban kasa tsige Buratai da ragowar Hafsun Sojojin Najeriya

Abin da ya hana Shugaban kasa tsige Buratai da ragowar Hafsun Sojojin Najeriya

- Garba Shehu ya maidawa masu kiran a sauke shugabannin sojoji martani

- Hadimin shugaban kasar yace babu dokar da ta wajabta canza hafsun tsaro

- Mutane sun dura kan mai magana da yawun shugaban kasar a dalilin haka

Mai magana da yawun bakin shugaban Najeriya, Malam Garba Shehu, ya yi magana game da kiran da ake yi na sauke shugabannin hafsun sojoji.

Garba Shehu ya bayyana cewa sauke shugabannin tsaron ya rataya ne a kan mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Da yake hira da gidan talabijin na TVC, hadimin shugaban kasar yace mutane su kyale mai gidan na sa ya sauya shugabannin tsaro a lokacin da ya ga dama.

A cewar Shehu, shugaban kasa Muhammadu Buhari yana cigaba da aiki da hafsun sojojin ne domin ya na ganin abin da sauran mutane ba su gani.

KU KARANTA: Miyagu sun tsere yayin da sojoji suka tarwatsa mafakarsu Kaduna

Da yake bayani a ranar Lahadi, hadimin na Muhammadu Buhari ya ce shugabannin sojojin sun a yi wa mai girma shugaban kasa aiki ne ba kowa ba.

Malam Shehu ya kuma kara da cewa: “Babu wata doka da ta ce dole sai an sauke hafsun sojoji bayan shekaru biyu.

“Shugaban kasa ya ce zai yi canji. Yaushe zai yi canjin? Ya rage na shi. Ina tunanin ya kamata mutanen Najeriya su yi masa kyakkyawan zato.” Inji Shehu.

Bayan wannan jawabi, kungiyar COCNE ta dattawan Najeriya ta caccaki Garba Shehu, ta ce kalaman hadimin abin kunya ne na wanda bai san aiki ba.

KU KARANTA: :Yan bindiga sun kashe mutane, sun tsere da dabbobi a Zamfara

Abin da ya hana Shugaban kasa tsige Buratai da ragowar Hafsun Sojojin Najeriya
Malam Garba Shehu Hoto: Facebook: GarShehu
Source: Facebook

COCNE tace bai kamata kwararren ‘dan jarida irin Garba Shehu ya yi irin wannan katabora na kare hafsun sojojin da su ka gaza kare al’umma.

A makon nan ne mu ka ji cewa 'yan ta'addan kungiyar Boko Haram sun kai hari, sun kona makaranta da wurin jinyar marasa lafiya a jihar Yobe.

An yi dace rundunar Sojoji sun yi ba-ta-kashi da ‘yan ta’adda bayan danyen harin garin Gujba.

Idan za ku tuna Kafin yanzu an kai hari a karamar hukumar Geidam, har an sace wani Basarake. Wannan ne hari na biyu da aka kai a jihar a makon jiya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel