Shugaban kasa 2023: Primate Ayodele ya ce Allah bai aiko Tinubu don ya shugabanci Najeriya ba

Shugaban kasa 2023: Primate Ayodele ya ce Allah bai aiko Tinubu don ya shugabanci Najeriya ba

- Wani shugaban addini, Primate Babatunde Elijah Ayodele, ya ce Allah ya sanar masa da wasu abubuwan da za su faru a 2021

- Malamin ya yi ikirarin cewa an sanar da shi abunda zai faru idan Bola Tinubu yayi yunkurin zama Shugaban kasa

- Primate Ayodele ya bayyana dalilin da yasa Allah baya goyon bayan yunkurin Tinubu na zama shugaban kasa

Zamowar Bola Tinubu, babban jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC), na zama Shugaban kasar Najeriya na gaba ba mai yiwuwa bane kamar yadda Primate Babatunde Elijah Ayodele ya kaddamar a wahayinsa.

Primate Ayodele, Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church da ke Lagas ya fada ma Legit TV a wata hira cewa Allah baya goyon bayan shugabancin Tinubu.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar APC ta yi zargin cewa majalisa na shirin tsige Buhari ta daura Osinbajo

A cewar faston, duk wani yunkuri da jigon na APC zai yi don takarar Shugaban kasa ba zai cimma nasara ba.

Ya ce:

“Shugabancin Tinubu zai sha kunya... saboda Allah bai aiko Tinubu don ya shugabanci Najeriya ba.”

KU KARANTA KUMA: Zargin tsokana: Dino Melaye ya fada ma Buhari cewa kada ya kama Bishop Kukah

A wani labarin, mun ji cewa kungiyar CAN ta Kiristocin Najeriya ta fito ta kare babban limaminta a Sokoto, Bishof Mathew Hassan Kukah.

Kungiyar ta CAN ta ce a jawabin da Mathew Hassan Kukah ya yi na bikin Kirismeti, babu inda ya soki Musulunci ko kuma ya yi kiran ayi juyin-mulki.

CAN ta zargi gwamnatin tarayya, shugaban kasa da kuma shugaban kungiyar MURIC, Farfesa Ishaq Akintola da neman juya maganar da Faston ya yi.

A gefe guda, Dino Melaye, tsohon sanata, ya gargadi Shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan yunkurin kama limamin Katolika na Sokoto, Mathew Kukah, kan sukar gwamnati mai ci.

Wasu kungiyoyi a kasar sun caccaki limamin kan zargin Shugaba Buhari da son kai.

Kungiyar matasan Tiv sun zargi limamin da kira ga tunkudar da shugaban kasar sannan suka bukaci hukumomin tsaro su binciki malamin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel