An kulla yarjejeniya tsakanin Buhari da Tinubu akan kujerar shugaban kasa

An kulla yarjejeniya tsakanin Buhari da Tinubu akan kujerar shugaban kasa

- Batun yankin da zai fitar da dan takarar shugaban kasa a shekarar 2023 na cigaba da yamutsa jam'iyyar APC

- Wasu jiga-jigan 'ya'yan jam'iyyar APC na ganin cewa arewa ce ya kamata ta cigaba da mulki

- A bangare guda kuma, wasu daga cikinsu na ganin cewa yankin kudancin Nigeria ne ya kamata takara ta koma a 2023

Babban kusa a jam'iyya mai mulki, APC, ya bayyana yadda aka kulla wata yarjejeniya da aka cimma tsakanin shugabannin jam'iyyar tun shekarar 2014, kamar yadda Punch ta rawaito.

Tunde Balogun, wanda shine shugaban rikon jam'iyyar a jihar Legas, ya bayyana cewa akwai yarjejeniyar baiwa Yarabawa mulki a shekarar 2023.

Ya ƙara da cewa, Buhari da Tinubu na cikin waɗanda suka amince da wannan yarjejeniya.

Shugaban ya bayyana haka ne a jihar Legas inda ya sanar da cewa shugabannin da suka kafa jam'iyyar APC a shekarar 2014 sun amince da tsarin mika wa shiyyar Yarabawa kujerar shugaban ƙasa bayan zango biyu na mulkin Buhari.

KARANTA: Bamu tuntubi kowa ba; Boko Haram ta dauki alhakin sace daliban Kankara a Katsina

An kulla yarjejeniya tsakanin Buhari da Tinubu akan kujerar shugaban kasa
An kulla yarjejeniya tsakanin Buhari da Tinubu akan kujerar shugaban kasa @APC Nigeria
Asali: Facebook

Bolagun ya bayyana hakan ne ga jaridar Punch tare da fadin cewa abin kunya ne ga shugabanninsu na APC su yi watsi da wannan yarjejeniya.

Yana wannan bayani ne a daidai lokacin da shugaba Buhari ya sauke wani hadimin jagoran jam'iyyar, Bola Tinubu, wato Farfesa Pondei, daga muƙamin shugabancin gudanarwa na hukumar NDDC.

KARANTA: Sakandire: Dalibai fiye da 500 sun koma makaranta dauke da juna biyu bayan hutun korona

A shafinsa na Tuwita, jagoran jam'iyyar, Asiwaju Bola Tinubu, ya yi wani rubutu dake nuna cewa wajibi ne a girmama yarjejeniyar 2014 na bawa yankin Yarabawa shugabancin kasar nan a 2023.

Wannan rubutu nasa ya janyo martani daga yan Najeriya musamman 'yan yankin kudu maso gabas, wato 'yan kabilar Igbo wadanda ke ikirarin cewa lokaci ne da su ma za'a ba su damar shugabancin ƙasar nan, ba wai Yarabawa da Hausa Fulani kadai ba.

A kwanakin baya ne Legit.ng Hausa ta rawaito shugaban riko na jam'iyyar APC, Mai Mala Buni, na cewa nan bada dadewa ba jam'iyyar APC za ta tashi wata guguwar siyasa da za ta girgiza Najeriya.

Buni ya bayyana hakan ne bayan gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi da Sanata Elisha Abbo daga jihar Adamawa sun sauya sheka daga PDP zuwa APC.

Shugabanni da jagororin jam'iyyar APC sun gana a sirrance da tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng