Za mu yi Tinubu kwanmu da kwarkwatarmu idan ya fito inji kungiyar BAT – GV

Za mu yi Tinubu kwanmu da kwarkwatarmu idan ya fito inji kungiyar BAT – GV

- Bola Ahmed Tinubu Grassroots Volunteers za ta goyi bayan Asiwaju Tinubu a 2023

- Kungiyar ta ce muddin ‘Dan siyasar ya tsaya takara a zabe, shi za ta marawa baya

- Shugaban BAT-GV, ya ce Tinubu bai da kabilanci, kuma ya na da son kawo cigaba

Wata kungiyar siyasa mai suna Bola Ahmed Tinubu Grassroots Volunteers, ta ce za ta goyi bayan jagoran na APC idan ya fito takara a zaben 2023.

Kungiyar BAT–GV ta fitar da jawabi ta na cewa idan har gwanin nata ya tsaya takarar shugaban kasa, za ta tashi tsaye wajen ganin ya yi nasara.

Jaridar Vanguard ta rahoto wannan jawabi da shugaban tafiyar Bola Ahmed Tinubu Grassroots Volunteers na kasa, Dozie Nwankodu, ya fitar.

Mista Dozie Nwankodu ya bayyana cewa suna tare da tsohon gwamnan na Legas ne domin kishin-kasa, ganin irin tarin cigaban da ya kawo.

KU KARANTA: 2023: Mutane miliyan 1 da za su marawa Bola Tinubu baya

Nwankodu ya ce babu ‘dan siyasa maras kabilanci irin jigon na APC, ganin yadda ya tafi da mutane daga ko ina lokacin da ya ke gwamnan Legas.

Shugaban wannan tafiya ya bayyana ‘dan siyasar a matsayin mai son cigaba da zaman lafiya.

Ya ce:

“Idan ku ka duba shugabannin da ake yi a baya da yanzu da irin gudumuwar da su ka ba jama’a, za ku ga Tinubu ne kurum ya yarda da kafa mutane.”

KU KARANTA: Siyasa ta sa an tunawa Tinubu abin da ya taba fada a 1997

Za mu yi Tinubu kwanmu da kwarkwatarmu idan ya fito inji kungiyar BAT – GV
Asiwaju Tinubu Hoto: www.thecable.ng
Source: Facebook

“Saboda gwagarmayarsu Tinubu ne ake cin romon mulkin farar hula a yau. Tinubu su ka tashi su ka ce dole sai sojoji sun mikawa farar hula mulki.”

A cewar Nwankodu, “Idan ka tsaya ka yi la’akari da kyau da abin da ya yi wa kasa, za ku fahimci cewa shi ne irin shugaban da Najeriya ke bukata.”

A jihar Kano, rikicin cikin gidan APC ya yi kamari har ta kai ‘Dan Majalisar Rimin-Gado da Dawakin Tofa ya yi wa Abdullahi Ganduje kaca-kaca.

Tijjani Abdulkadir Jobe ya jefawa Abdullahi Ganduje da shugabannin APC a Kano kalubale.

‘Dan Majalisar da ya fito daga Mahaifar gwamnan ya caccaki jagororin APC a jihar Kano, ya ce babu wanda ya isa ya yi sanadiyyar da zai sauya-sheka.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel