Siyasar Kano: Babu wanda ya isa ya kore ni daga jam’iyyar APC inji Hon. Jobe

Siyasar Kano: Babu wanda ya isa ya kore ni daga jam’iyyar APC inji Hon. Jobe

- ya soki Gwamna Abdullahi Ganduje da manyan APC

- . J ya na wakiltar / , amma an ja layi a APC

- ‘Dan Majalisar ya kira Gwamna barawo, ya kuma ce bai jin tsoron kowa

Honarabul Abdulkadir Jobe mai wakiltar mazabar Dawakin Tofa da Rimin Gado a majalisar tarayya, ya fito ya na sukar gwamna Abdullahi Ganduje.

A wani bidiyo da aka wallafa a shafin Twitter, an ji Abdulkadir Jobe ya na yin kaca-kaca da mai girma gwamnan, har ya na kiransa da sunaye maras dadi

Jobe ya yi kaca-kaca da masu yi masa barazana, ya ce babu wanda ya isa ya kore sa daga jam’iyya.

A wannan bidiyo da wani mai suna Hassan Umar ya wallafa a ranar 3 ga watan Junairu, 2020, an ji mabiya bayan Jobe su na yi masa kirarin ‘daram-dam.”

KU KARANTA: Shugabannin majalisar dokokin jihar Kano sun yi murabus

Saboda haka, ni ‘Dan jam’iyyar APC ne cikakke, mu na nan a APC, a APC babu wanda ya isa ya kore ni daga jam’iyya

Jobe ya aika sakonsa na musamman zuwa ga Abdullahi Umar Ganduje, ya na ce masa ‘Kai barawo ne!’

Wasu a gefe sun amsa da cewa: (Gwamna) ya ci Dala. An dade ana zargin gwamnan Kano. Dr. Abdullahi Ganduje da laifin karbar rashawan Daloli.

Hon. Abdulkadir Jobe ya ke cewa ‘dan majalisar da ya fito daga kudancin jihar Kano ya ce: “Ina alfahari da kaina, da iyayena, da mutanen garin Dawakin Tofa.”

KU KARANTA: Tinubu, Zulum, El-Rufai, da sauran ‘Yan siyasa 7 da za a saurara a 2020

Siyasar Kano: Babu wanda ya isa ya kore ni daga jam’iyyar APC inji Hon. Jobe
Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje Hoto: Twitter daga: @GovUmarGanduje
Source: Twitter

‘Dan siyasar ya yi ikirarin su ne masu jama’a. “Ko za a mutu, ko za ayi rai, mu na APC. Idan mutum ya ce shi ‘dan APC ne, ko waye shi, ya tsaya a fito ayi zabe.”

A karshen wannan bidiyo, za a ji ‘dan majalisar ya na cewa ya lashe zaben majalisar tarayya har sau uku: “Kowa ya san ni, ya sanni Jobe, ba mai tsoro ba ne.”

Kwanaki kun ji cewa an yi hannun riga tsakanin Abdullahi Umar Ganduje da Sha'aban Sharada, mai wakiltar mazabar Birnin Kano a majalisar wakilai na kasa.

Tsohon hadimin shugaban kasar Najeriyar ya ajiye alakar jam'iyyar APC, ya zargi gwamnatin Abdullahi Ganduje da saida kadarorin gwamnatin jihar Kano.

Sha'aban Sharada ya na cikin 'ya 'yan APC da su ka samu sabani da Abdullahi Ganduje a Kano.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel