Ban yarda da Najeriya ‘kasa daya’ ba – An tunawa Tinubu abin da ya fada a 1997
Wata magana da tsohon gwamnan Legas, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya taba yi ta na nema ta jawo masa matsala musamman a yanzu da ya ke siyasar kasa.
A wata hira da ya taba yi da jaridar This Day a ranar 13 ga watan Afrilu, 1997, Cif Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa bai yarda cewa Najeriya kasa daya ce ba.
Wadannan kalamai na ‘dan siyasar sun dawo su na yi masa illa, ganin cewa ana rade-radin ya na cikin masu harin takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2023 a APC.
A tsakiyar makon nan aka bankado wannan tsohuwar jarida, hakan ya sa mutane su ke mamakin yadda mutumin da bai yi amanna da shimfidar Najeriya zai mulke ta ba.
Jaridar Daily Nigerian ta tattaro wasu daga cikin martanin mutane a shafukan sada zumunta inda aka ji da-dama su na sukar babban jagoran na jam’iyyar APC mai mulki.
Shararren Farfesan nan Farooq Kperogi, ya yi kaca-kaca da ‘dan siyasar, ya na cewa: “’Yan siyasar Najeriya ba su da kunya, sai kishin kasar karya.” A karshe ya ce: “Mutumin da bai yarda da shimfidar Najeriya ba a lokacin da bai da ta-cewa, ya na so ya jagorance ta yanzu. Kaico!”
KU KARANTA: Babban yaron Amaechi ya bar APC, ya hada-kai da Gwamna Wike
Wani @RealThunderClap, ya rubuta: “TINUBU da bai yarda da Najeriya kasa daya ba, amma ya na so ya zama shugabanta.
Ni hankali na kwance tuni domin na san wadannan tarkacen da aka kira shugabanni a Najeriya, masu neman na-abinci ne kurum, ba su da wata akida ko manufa, balle daraja…abin da ke gabansu shi ne tuwo da lomar da za su samu. Tir.
“13 ga watan Afrilu, 1997, Tinubu ya ce bai yarda Najeriya kasa daya ba ce, amma bayan ya wawuri dukiyar jihar Legas daga 1999 zuwa yau, ya fara buga kalangun Najeriya." Inji Simon Ekpa.
Shi kuma @SodiqTade ya rubuta: “Na tuna yadda irinsu Lai, Tinubu, Bakare su ka yi wa Buhari kwaskwarima da kayan turawa a wancan shekara.”
Irinsu @Oyeleke4 su na ganin Tinubu bai yi laifi ba, domin ya yi wannan magana ne lokacin da Janar Sani Abacha ya huro masu wuta har su ka tsere daga kasar.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng