An samu Mutane miliyan 1 da za su marawa Bola Tinubu baya a zaben 2023

An samu Mutane miliyan 1 da za su marawa Bola Tinubu baya a zaben 2023

Wata kungiyar siyasa da ta ke neman jagoran jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya fito takarar shugaban kasa a zaben 2023, ta samu masoya miliyan guda a halin yanzu.

A ranar Litinin, 20 ga watan Yuli, jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto cewa ana hurowa tsohon gwamnan Legas ya nemi takara domin ya gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Duk da wannan kururuwa da ake ta yi, har yanzu tsohon gwamnan bai yanke hukuncin tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023 ba, ganin cewa akwai sauran lokaci tukuna.

Bola Tinubu ya taba bayyana cewa abin da ke gabansa ayanzu shi ne yadda zai ba gwamnatin shugaba Buhari shawarwarin yadda za ta kai ga nasara ba wai siyasar 2023 ba.

Kungiyar Tinubu 2023, Not Negotiable wanda aka fi sani da TNN, ta yi bikin cika shekara guda kwanan nan, ta kuma bayyana cewa ta na kara samun magoya baya har a kasashen waje.

Shugaban TNN, Hon. Kunle Okunola ya ce kungiyar ta su ta shiga kasashen Duniya 13 – Faransa, Birtaniya, da kuma wasu kasashen Afrika.

KU KARANTA: Tsohon jagoran majalisa ya bar PDP, ya koma APC

An samu Mutane miliyan 1 da za su marawa Bola Tinubu baya a zaben 2023
Bola Tinubu da Atiku fa Fintiri
Asali: Facebook

TNN ta na kokarin ganin takarar Asiwaju Bola Tinubu ta tabbata a 2023.

Jaridar ta yi magana da wani tsohon jigon PDP wanda yanzu ya koma tafiyar APC, Mutiu Okunola, wanda ya bayyana cewa a 2023, babu abin da zai hana Bola Tinubu zama shugaban kasa.

Okunola ya ce bayan Tinubu ya cancanci ya rike kasar, shi kadai ne wanda zai iya jawo ra’ayin 'yan babu ruwa nan siyasa, kuma wanda zai iya kai Najeriya ga ci idan ya samu mulki

A cewar tsohon jagoran na PDP, wasu sun fara kokarin yi wa Bola Tinubu zagon-kasa, amma a cewarsa, wannan yunkuri da ake yi ba zai hana ‘dan siyasar kai labari ba.

Magoya bayan Tinubu su na hada kai da manyan ‘yan siyasan Arewa da na Kudancin kasar da tsofaffin ‘yan jam’iyyar APC da magoya bayan shugaba Buhari domin cin ma wannan nufi.

Hon. Dipo Olounrinu wanda ya na cikin manyan APC a Legas, ya yi kira ga ‘yan Najeriya su bada goyon bayansu ga Tinubu a lokacin da ya fito takara.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng